Wakokin JW

Ka ji dadin saurarar wakokin da suke nuna godiyarmu ga Jehobah.

Ka Dauka Muna Aljanna

Sabuwar rayuwa a Aljanna tana jiran mu a nan gaba.

Aljanna Ta Kusa

Idan muna sa rai ga aljanna da ta kusan zuwa, zai taimaka mana mu jimre.

Ku Yi Zabin da Zai Faranta Ran Jehobah

Ku yi zabin da zai faranta ma Jehobah rai a kowace rana.

Bangaskiya Za Ta Sa Mu Cim ma Kome

Sai mun sa kokari sosai kafin mu iya gina bangaskiya mai karfi, amma idan mun ya hakan Jehobah zai yi mana albarka.

Ina Bin Dokokinka

Mu rika nunawa ta ayyukanmu da halayenmu cewa muna son dokokin Jehobah sosai.

Zan Sake Tashi

Ku ga yadda wata ʼyar’uwa da ta daina halartar taro ta sake soma halarta.

Ayyukanka Na da Ban Al’ajabi

Ka dauki gatanka na yin aikin tare da Jehobah da muhimmanci!

ʼYar Kirki

Wani mahaifi ya ga sa’ad da ʼyarsa ta yi girma kuma ta soma bauta wa jehobah.

Mu Fara Hidimar Majagaba

Idan muna inganta hidimarmu a ta kowane fanni, hakan zai sa mu yi murna a matsayinmu na bayin Allah.

Ka Kalle Ni

Mu yi iya kokari don mu amfana daga tarayyar da muke yi da ’yan’uwanmu.

Halittunka Suna da Ban Mamaki

Abubuwan da Jehobah ya halitta suna da ban mamaki, shi ya sa muke masa yabo.

Abubuwa Masu Muhimmanci

Ya dace mu kebe lokaci da za mu rika yin addu’a da nazari da kuma ayyukan ibada.

Soyayya Ruwan Zuma

Bin umurnin Jehobah game da aure zai taimaka muku ku ji dadin aurenku!

Wurin da Zai Sa A Yabe Ka

Babban gata ne a gare mu mu gina wannan gidan da zai sa a rika daukaka sunansa.

Na Dogara da Kai

Karanta da kuma yin bimbini a kan Kalmar Allah za su taimaka mana sa’ad da muke fuskantar matsaloli.

Zan Canja Hanyoyin Wa’azina

Shin an taba karfafa ka ka canja yadda kake wa’azi?

Kauna ta Kirista

Mutanen Jehobah suna taimaka wa juna sa’ad da muka shiga cikin matsala.

Kar Ka Ji Tsoro

Idan muna fama da matsaloli, muna bukatar mu tuna cewa Allah yana tare da mu.

Neman Gaskiya

Wadanda suke son su san game da Allah za su iya yin hakan idan suka yi kokari sosai wajen neman gaskiya game da shi.

Abokan Kwarai

Amma a ina za mu iya samun abokan kirki?

Zan Kasance da Kai

Za mu iya dogara ga abokan kirki a lokacin da muke cikin matsala.

Mu Bayin Jehobah Muna da Hadin Kai

Duk da yake ba salma a duniya, mu Shaidun Jehobah muna da salama da kuma hadin kai da juna.

Ka Ba Ni Karfin Hali

Jehobah zai ba mu karfin zuciya don iya jimre duk wani jarabawa da muke fuskanta.

Zan Bauta Maka

Jehobah ya cancanci mu bauta masa da dukan zuciyarmu.

Kowace Rana da Matsalolinta

Za mu iya yin farin ciki duk da matsalolinmu.

Yi Karfin Zuciya

Wakar da za ta taimaka mana mu jimre matsaloli.

Zan Maka Godiya

Ka dau lokaci ka yi tunani a kan abubuwan da Allah ya halitta, sai ka gode masa a cikin addu’a.

Mu Iyali Ne

Ko a ina muke, muna cikin iyalin Jehobah.

Ku Yi “Tsere Na Bangaskiya”

Duk da matsalolin da muke fama da su, za mu iya kasance da aminci ga Jehobah.

Jehobah Yana Tare da Mu Kullum

Jehobah yana a shirye ya rika taimaka mana.

Rayuwa a Cikin Aljanna

Abubuwan da muke tunani ne suke shafan mu. Wannan wakar za ta taimaka mana mu mai da hankali ga sabuwar duniya.

Na Ba Jehobah Rayuwata

Kaunar da muke yi wa Jehobah ne take sa mu yi alkawarin bauta masa kuma mu yi baftisma.

Kauna Ba Ta Karewa

Kaunar Jehobah ba ta karewa. Tana sa mu farin ciki da kuma ƙarfafa mu.

Mu Gaya Masa Damuwarmu

Idan kana bakin cikin, ka dogara ga Jehobah don ya karfafa da kuma ta’azantar da kai.

Mu Zama Kamar Yara

Ta yaya za mu nuna kauna kamar yadda yara suke yi?

Ku Zama da Tabbaci

Muna da tabbaci cewa Jehobah yana kaunar mu duk da matsalolin da muke fuskanta.

Ku Rika Gafartawa

Wani ya taba bata maka rai? Shin yana maka wuya ka gafarta masa? Ka ga yadda za ka iya gafartawa.

Mu Yi Tsere

Ka tsai da shawarwari masu kyau don ka ci gasar tsere na rai na har abada.

Ba Za Mu Daina Bauta wa Jehobah Ba

Kasancewa da bangaskiya mai karfi yana kamar gina gida mai karfi.

Rabin Raina

Ku more kyautar Jehobah na aure.

Ka Kiyaye Zuciyarka

Da taimakon Jehobah, za ka iya daina yawan damuwa.

Mu Yi Murna Koyaushe

Waka mai dadi tana iya sa mu tuna da dalilan yin farin ciki a rayuwa.

Muna da Hadin Kai

Duk da matsaloli da kuma tsanantawar da ake mana, mun ci gaba da kasancewa da hadin kai.

Ku Yi Amfani da Karfinku a Hidimar Jehobah

Ka yi amfani da karfinka a hidimar Jehobah. Ba za ka yi da-na-sani ba!

Jehobah ne Ke Sa Mu Farin Ciki

Jehobah a kullum yana sa mu farin ciki.

Ku Zo Ku Ga Aljannar

Ku yi farin ciki don alkawarin da aka yi mana na sabuwar duniya.

Mu Yi Kusa da Jehobah

Rayuwa mafi kyau ita ce mutum ya shagala a ayyukan ibada.

Mu Zama da Bangaskiya

Ka yi tunanin irin rayuwa mai kyau da Allah yake shirya mana a nan gaba.

Iyalin Jehobah

Akwai mutanen da suke neman su san gaskiya game da Allah. Bidiyon nan zai sa ka kara kwazo wajen neman irin mutanen nan.

Mu Kulla Zumunci

Da taimakon Jehobah da kuma ꞌyanꞌuwanmu, za mu iya jimre kowane irin matsala.

Gun Waye Zan Je?

Mu bauta wa Jehobah da aminci a dukan rayuwarmu, kuma mu saurari muryar makiyayinmu.

Ba Zan Ji Tsoro Ba

Za mu iya shawo kan duk wani tsoro da taimakon Jehobah.

Mu Sasanta

Ka yafe duk wata laifin da aka yi maka kuma ka yi zaman lafiya da mutane!

Ka Komo Gun Jehobah

Idan ka yi kuskure kuma ka yi gyara, za ka zama aminin Jehobah kuma.

Tuna Aljanna

Za mu iya samun farin ciki da gamsarwa a rayuwarmu yanzu da kuma a nan gaba.

Salama Za Ta Zo (Wakar Taron Yanki na 2022)

Bari alkawarin Allah cewa zai kawo salama ya karfafa ka.

Mu Yi Kusa da Shi

Allah yana son dukan wandada suke so su kusace shi, ko daga ina ne suka fito.

“Ba Zai Yi Latti Ba!” (Wakar Taron Yanki na 2023)

Yayin da kake jiran lokacin Jehobah, ka yi koyi da mutanen da masu aminci.