Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 79

Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

Mu Koya Musu Su Kasance da Aminci

(Matta 28:​19, 20)

  1. 1. Tumakin Jehobah Allahnmu

    Sun girma, muna murna.

    Allah ya kula da su sosai

    Don suna bauta masa.

    (AMSHI)

    Jehobah ka ji roƙonmu

    Ka kuma kāre su sosai.

    Mun roƙa ta sunan Yesu Don su tsira,

    Su kuma riƙe aminci.

  2. 2. Muna yin addu’a dominsu,

    Ba ma so su karaya.

    A kullum muna koyar da su,

    Hakan ya ƙarfafa su.

    (AMSHI)

    Jehobah ka ji roƙonmu

    Ka kuma kāre su sosai.

    Mun roƙa ta sunan Yesu Don su tsira,

    Su kuma riƙe aminci.

  3. 3. Ka sa duk su dogara da kai,

    Da kuma Ɗanka Kristi.

    Su jimre su fa yi biyayya,

    Don su tsira da ransu.

    (AMSHI)

    Jehobah ka ji roƙonmu

    Ka kuma kāre su sosai.

    Mun roƙa ta sunan Yesu Don su tsira,

    Su kuma riƙe aminci.

(Ka kuma duba Luk. 6:48; A. M. 5:42; Filib. 4:1.)