Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Amsoshin Tambayoyin Masu Karatu

Ta yaya “Urushalima” da aka ambata a Ishaya 60:1 ta “tashi” kuma ta “haskaka”?

Ishaya 60:1 ta ce: “Tashi ki haskaka, ya ke Urushalima, gama haskenki ya zo! Gama ɗaukakar Yahweh tana haskakawa a kanki!” Urushalima ita ce babbar birnin ƙasar Yahuda, kuma tana wakiltar dukan ƙasar. (Isha. 60:14; 62:1, 2) Annabcin nan da Ishaya ya yi ya ta da tambayoyi guda biyu: Ta farko, a wane lokaci ne Urushalima ta “tashi” ta haskaka, kuma ta yaya ta yi hakan? Ta biyu, annabcin yana cika a zamaninmu?

A wane lokaci ne Urushalima ta “tashi” ta haskaka, kuma ta yaya ta yi haka? Urushalima ta zama kufai a lokacin da Yahudawa suka yi shekaru 70 suna zaman bauta a ƙasar Babila. Amma da mutanen Midiya da Fasiya suka ci ƙasar Babila da yaƙi, sun ba Israꞌilawa ꞌyanci su koma ƙasarsu don su maido da bauta ta gaskiya. (Ezra 1:1-4) A shekara ta 537 kafin haihuwar Yesu ne Israꞌilawa masu aminci suka fara komawa ƙasarsu. (Isha. 60:4) Da zuwan su, sun soma miƙa hadayu, da yin bukukuwa da kuma gina haikalin Jehobah. (Ezra 3:1-4, 7-11; 6:16-22) Yadda aka yi ke nan ɗaukakar Jehobah ta sake haskakawa a kan Urushalima, wato mutanensa. Da yake ƙasashen da ke kewaye da su ba su san Jehobah ba, kamar dai suna cikin duhu ne, kuma Israꞌilawan sun zama musu haske.

Amma Israꞌilawan ba su ci-gaba da haskakawa kamar yadda Jehobah ya so ba. Don haka, annabcin bai gama cika a zamaninsu ba. Daga baya yawancinsu sun yi wa Allah rashin biyayya. (Neh. 13:27; Mal. 1:6-8; 2:13, 14; Mat. 15:7-9) Sun ma ƙi su yarda da Almasihu. (Mat. 27:1, 2) Kuma an sake halaka Urushalima da haikalinta a shekara ta 70 bayan haihuwar Yesu.

Tun dā ma Jehobah ya ce hakan zai faru. (Dan. 9:24-27) Don haka, ya san cewa Urushalima ta zahiri ba za ta cika annabcin da ke Ishaya sura 60 gabaki ɗaya ba.

Annabcin Ishaya yana cika a zamaninmu ma? E, amma a maimakon annabcin ya cika a Urushalima ta zahiri, yana cika ne a “Urushalima ta sama.” Manzo Bulus ya yi magana game da ita cewa: “Ita ce mamarmu.” (Gal. 4:26) Urushalima ta sama tana nufin sashen ƙungiyar Jehobah da ke sama, da ta ƙunshi malaꞌiku masu aminci. A cikin ꞌyaꞌyanta, akwai Yesu da shafaffun Kiristoci kamar manzo Bulus, da za su yi rayuwa a sama. Shafaffun Kiristocin nan “alꞌumma ce mai tsarki,” su ne “Israꞌila ta Allah.”—1 Bit. 2:9; Gal. 6:16.

Ta yaya Urushalima ta sama ta “tashi” kuma ta “haskaka”? Ta yi hakan ne ta wurin ꞌyaꞌyanta shafaffu da ke nan duniya. Bari mu ga yadda abubuwan da suka faru da su suka yi daidai da annabcin da aka yi a Ishaya sura 60.

Bayan mutuwar manzannin Yesu, ꞌyan ridda sun yaɗa koyarwar ƙarya kuma hakan ya sa Kiristocin ƙarya sun mamaye Kiristoci na gaske. Shi ya sa Kiristoci na gaske suke bukatar su sake “tashi.” (Mat. 13:37-43) Kafin Kiristoci na gasken su tashi, suna ƙarƙashin ikon Babila babba, wato daular addinin ƙarya. Sun ci-gaba da zama a ƙarƙashin addinin ƙarya har 1914, wato shekarar da “ƙarshen duniya” ya soma. (Mat. 13:39, 40) A shekara ta 1919, sun sami ꞌyanci daga addinin ƙarya, kuma suka soma yin waꞌazi. Ta haka ne suka soma haskakawa. a Tun daga lokacin, mutane daga dukan ƙasashe sun yi ta zuwa wurin haskenta, har da sauran mutanen Israꞌila ta Allah, waɗanda su ne “sarakuna” da aka yi zancen su a Ishaya 60:3.—R. Yar. 5:9, 10.

A nan gaba, shafaffun Kiristoci za su haskaka fiye da hakan. Ta yaya? Idan suka gama hidimarsu a nan duniya, za su haɗu da shafaffu da ke sama su zama “Sabuwar Urushalima,” wadda ita ce amaryar Kristi, wato shafaffu 144,000 da za su zama sarakuna da kuma firistoci tare da Yesu.—R. Yar. 14:1; 21:1, 2, 24; 22:3-5.

Sabuwar Urushalima za ta taka rawar gani sosai wajen cika annabcin da ke Ishaya 60:1. (Ka duba alaƙar da ke tsakanin Ishaya 60:1, 1, 3, 5, 11, 19, 20 da Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 21:2, 9-11, 22-26.) Urushalima ta zahiri ce cibiyar gwamnatin ƙasar Israꞌila ta dā. Haka ma, Yesu Kristi da Sabuwar Urushalima za su zama cibiyar Gwamnati da Allah zai kafa. Me ake nufi da cewa Sabuwar Urushalima za ta ‘sauko daga sama daga wurin Allah’? Hakan yana nufin cewa za su mai da hankali ga duniya. Masu tsoron Allah daga dukan alꞌummai “za su yi tafiya” a cikin “haskensa.” Ba za su sake yin zunubi ko su mutu ba. (R. Yar. 21:3, 4, 24) A ƙarshe, “za a mai da dukan abubuwa sabo,” kamar yadda annabi Ishaya da wasu annabawa suka faɗa. (A. M. 3:21) An fara mai da abubuwa sabo saꞌad da Yesu ya zama Sarki, kuma za a gama a ƙarshen Sarautarsa na Shekara Dubu.

a Ezekiyel 37:1-14 da Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 11:7-12 sun annabta yadda za a maido da bauta ta gaskiya a 1919. Ezekiyel ya annabta yadda za a ꞌyantar da dukan shafaffun Kiristoci daga bauta da suka daɗe suna yi. Littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna kuma, ya yi bayani a kan yadda wani ƙaramin rukunin shafaffun Kiristoci da suke ja-goranci za su sake tashi. Dā ma an rufe su a kurkuku kuma hakan ya hana su bauta ma Jehobah yadda suka saba. Amma daga baya an sake su, kuma abin da annabcin yake nufi da cewa sun sake tashi ke nan. A 1919 ne aka mai da su “bawan nan mai aminci, mai hikima.”—Mat. 24:45; ka duba shafi na 118 na littafin nan, Pure Worship of Jehovah—Restored At Last!