Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Mene Ne Nufin Allah Ga Mutane?

Mene Ne Nufin Allah Ga Mutane?

Allah yana so mu zauna lafiya, cike da farin ciki a Aljanna a duniya, har abada!

Amma, kana iya cewa, ‘Hakan ba zai yiwu ba!’ Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa hakan zai yiwu a ƙarƙashin Mulkin Allah, kuma Allah yana so dukan mutane su koya game da wannan Mulkin da kuma nufin Allah a gare mu.—Zabura 37:11, 29; Ishaya 9:7.

Allah yana so mu amfana.

Kamar yadda mahaifin kirki yake yi wa ’ya’yansa fatan alheri, hakazalika, Ubanmu na sama yana so mu kasance masu farin ciki har abada. (Ishaya 48:17, 18) Ya yi alkawari cewa duk ‘wanda ya yi nufin Allah zai zauna har abada.’—1 Yohanna 2:17.

Allah yana so mu bi tafarkinsa.

In ji Littafi Mai Tsarki, Mahaliccinmu yana so ya “koya mana tafarkunsa” domin mu yi “tafiya cikin hanyoyinsa.” (Ishaya 2:2, 3) Allah ya tsara ‘wata jama’a domin sunansa,’ wadda za ta sanar da nufinsa a faɗin duniya.—Ayyukan Manzanni 15:14.

Allah yana so mu bauta masa cikin haɗin kai.

Maimakon ta jawo rashin jituwa a tsakanin mutane, bauta mai tsarki da muke yi wa Jehobah tana sa mutane su kasance da haɗin kai kuma su so juna. (Yohanna 13:35) Su wane ne a yau suke koya wa maza da mata a ko’ina yadda za su bauta wa Allah cikin haɗin kai? Muna ƙarfafa ka ka bincika amsar wannan tambayar a cikin ƙasidar nan.