Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 2

Why Are We Called Jehovah’s Witnesses?

Why Are We Called Jehovah’s Witnesses?

Nuhu

Ibrahim da Saratu

Musa

Yesu Kristi

Mutane da yawa suna tunanin cewa Shaidun Jehobah sunan wani sabon addini ne. Amma, shekaru sama da 2,700 da suka shige, an kwatanta bayin Allah makaɗaici mai gaskiya a matsayin ‘shaidunsa.’ (Ishaya 43:10-12) Kafin shekara ta 1931, an san mu da sunan nan Ɗaliban Littafi Mai Tsarki. Me ya sa muka soma amfani da sunan nan Shaidun Jehobah?

Sunan yana bayyana ko wane ne Allahnmu. Rubutu na dā na Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa sunan Allah, Jehobah, ya bayyana fiye da sau dubu bakwai a cikin Littafi Mai Tsarki. An sauya wannan sunan da laƙabi kamar Ubangiji ko kuma Allah a cikin fassarar Littafi Mai Tsarki da yawa. Amma, tun dā can sa’ad da Allah yake bayyana kansa, ya gaya wa Musa cewa sunansa Jehobah, ko Yahweh in ji wasu fassarar Littafi Mai Tsarki, kuma ya ce: “Wannan shi ne sunana har abada.” (Fitowa 3:15) Ta hakan, Ya bambanta kansa daga dukan allolin ƙarya. Muna alfahari cewa muna amsa suna mai tsarki na Allah.

Sunan yana kwatanta aikin da muke yi. Tun daga zamanin Habila, adali na farko, mutane da yawa sun yi wa’azi game da bangaskiyarsu ga Jehobah. Da shigewar shekaru, mutane kamar su Nuhu da Ibrahim da Saratu da Musa da Dauda da dai sauran su, sun kasance cikin wannan “taron shaidu mai girma.” (Ibraniyawa 11:4–12:1) Kamar yadda mutum zai iya ba da shaida a kotu a madadin wani marar laifi, mun ƙudura mu bayyana gaskiya game da Allahnmu.

Muna yin koyi ne da Yesu. Littafi Mai Tsarki ya kira shi “amintaccen mashaidi mai-gaskiya.” (Ru’ya ta Yohanna 3:14) Yesu ya ce ya ‘sanar da sunan Allah’ kuma ya ci gaba da ‘ba da shaida ga gaskiya’ game da Allah. (Yohanna 17:26; 18:37) Saboda haka, wajibi ne mabiyan Kristi na gaskiya su kasance mutanen da suke amsa sunan Jehobah, kuma su sanar da sunan ga mutane. Abin da Shaidun Jehobah suke yi ke nan.

  • Me ya sa Ɗaliban Littafi Mai Tsarki suka soma amfani da sunan nan, Shaidun Jehobah?

  • A wane lokaci ne Jehobah ya soma samun shaidu a duniya?

  • Wane ne “amintaccen mashaidi mai gaskiya”?