Koma ka ga abin da ke ciki

Ta Wurin Mutum Daya An Fara Nazari da Mutane da Yawa

Ta Wurin Mutum Daya An Fara Nazari da Mutane da Yawa

 Wata Mashaidiyar Jehobah mai suna Marta, da take zama a kasar Guatemala, tana koyan yaren Kekchi don ta yi wa mutanen da ke yaren waꞌazi. Wata rana ta ga wani mutum ya fito daga wani asibiti. Da ganin shi sai ta gaya wa kanta cewa watakila ya fito ne daga wani kauyen da ake yaren Kekchi, inda Shaidun Jehobah ba sa cika zuwa waꞌazi. Sai ta je ta same shi, ta dan yi masa magana da yaren Kekchi duk da cewa ba ta jin yaren sosai.

 Marta ta tambayi mutumin ko zai so a yi nazarin Littafi Mai Tsarki da shi. Ya yarda amma ya ce mata ba ya da kudin da zai biya don nazarin. Marta ta bayyana masa cewa Shaidun Jehobah suna nazari da mutane kyauta. Kari ga haka, ta ce masa za ta iya yin nazari da shi da kuma iyalinsa gaba daya ta wajen wayar tarho. Mutumin ya yarda. Da yake ya iya yaren Sifanisanci kuma yana karanta yaren, ta ba shi Littafi Mai Tsarki juyin New World Translation of the Holy Scriptures na yaren Sifanisanci. Ta kara masa da littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa?, a yaren Kekchi. Bayan ꞌyan kwanaki sai Marta ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki ta wajen tarho da mutumin da matarsa da kuma yaransu biyu sau biyu a mako. Marta ta ce: “Da yake ban iya yaren Kekchi sosai ba, mukan yi nazarin da Sifanisanci saꞌan nan mutumin ya fassara abin da nake fada wa matarsa da yaren Kekchi. Yaran suna jin Sifanisanci.”

 Da yake mutumin fasto ne a cocinsa, sai ya soma koya wa ꞌyan cocinsa abin da yake koya daga nazarin da ake yi da shi. ꞌYan cocin sun ji dadin abin da yake gaya musu sai suka tambaye shi ina ne yake koyan sabbin abubuwan nan. Da ya gaya musu cewa ana nazarin Littafi Mai Tsarki da shi sai suka soma halartan nazarin daya bayan daya. Ba da dadewa ba sai wajen mutum 15 suka soma taruwa don Marta ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da su ta waya. Da shigewar lokaci, sun fara ajiye makarufo kusa da wayar domin kowa ya ji abin da ake tattaunawa da kyau.

 Saꞌad da Marta ta gaya wa dattawan ikilisiyarsu game da nazarin, sai daya daga cikin dattawan ya ziyarci kauyen da daliban suke zama. Dattijon ya gayyace su su je su saurari jawabin da wani mai kula da daꞌira a zai bayar a wani kauye mai nisa sosai. Daga inda daliban suke, zuwa kauyen zai dauke su awa daya a mota, saꞌan nan za su taka na tsawon awa biyu kafin su isa. Daliban sun yarda su halarci taron kuma guda 17 daga cikin su sun halarta.

 Makonni bayan haka, mai kula da daꞌirar da wasu Shaidu sun je kauyen da daliban suke kuma suka yi kwana hudu tare da su. Da safe, sukan kalli bidiyoyin Shaidun Jehobah a yaren Kekchi da ke jw.org, sai su yi nazarin kasidar nan Su Wane Ne Suke Yin Nufin Jehobah A Yau? Da rana kuma sukan kalli bidiyoyi a tashar JW. Mai kula da daꞌirar ya shirya yadda kowannensu zai sami danꞌuwa ko ꞌyarꞌuwa da za ta yi nazari da su.

 A cikin kwanaki hudun, Shaidun sun yi waꞌazi a kauyukan da ke kusa da su da ake yaren Kekchi kuma sun gayyace mutane a wurin zuwa wani taro na musamman. Mutane 47 suka halarci taron kuma ꞌyanꞌuwan sun tambaye su ko za su yarda a yi nazari da kowannensu. Iyalai sha daya sun yarda a yi nazari da su.

 Bayan ꞌyan watanni, dattawan sun shirya a yi taro a kauyen faston kowane karshen mako. A yau, wajen mutane 40 ne suke zuwa taro a kai a kai a kauyen. Kuma a lokacin da ꞌyanꞌuwan suka yi taron Tunawa da Mutuwar Yesu a kauyen, mutane 91 sun halarta. Hakan ya sa ꞌyanꞌuwan farin ciki sosai.

 Da Marta ta tuna yadda labarin ya fara da kuma abubuwa da suka faru daga baya, sai ta ce: “Ina godiya ga Jehobah. A wasu lokuta, nakan ji kamar ba na yin abubuwa da yawa a ibadata ga Jehobah. Amma Jehobah zai iya amfani da mu ya taimaka ma wasu. Ya san abin da ke zuciyar mutanen kauyukan shi ya sa ya jawo su zuwa wurin mutanensa. Jehobah yana kaunarsu.”

a Mai kula da daꞌira wani mai hidima ne na Shaidun Jehobah da yake ziyartar ikilisiyoyi wajen 20 a cikin daꞌira daya.