Koma ka ga abin da ke ciki

Bayanai a Karkashin Injin Wanki

Bayanai a Karkashin Injin Wanki

 Bayan wata mai suna Zarina ta yi baftisma a matsayin Mashaidiyar Jehobah, ta bar kasar Rasha kuma ta koma kasarsu a Asiya ta Tsakiya. Ta yi hakan ne domin tana son ta taimaka wa yaranta su koya game da Jehobah. Amma matsalar kudi ya sa ta koma zama da iyayenta da dan’uwan ta da matarsa a gida mai daki daya. Iyayenta sun umurce ta kada ta yi nazarin Littafi Mai Tsarki da yaranta mata biyu. Kuma suka gaya wa yaran kada su tattauna game da Littafi Mai Tsarki da mahaifiyarsu.

 Zarina ta yi tunanin yadda za ta taimaka wa yaranta su koya game da Jehobah. (Karin Magana 1:⁠8) Sai ta yi addu’a ga Jehobah don ya taimaka mata kuma ya ba ta hikima. Zarina ta soma fita yawo da yaranta kuma sa’ad suke hakan tana koya musu game da abubuwan da Allah ya halitta. Yin hakan ya sa yaran su soma sha’awar sanin abubuwa game da Mahalicci.

 Kari ga haka, Zarina ta nemi hanyar yin nazari da yaranta da littafi nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? a Takan kofi wasu sakin layi da ke cikin takardan har da tambayoyin a fallayen takarda. Sai ta dan rubuta karin bayani don ta taimaka wa yaranta su fahinci abin da ke fallayen. Sai ta boye fallayen takardun tare da fensir a dakin wanki a karkashin injin wanke kaya. Sa’ad da yaran suke wurin wankin sai su karanta kuma su rubuta amsar tambayoyin.

 Ta wajen yin amfani da wannan dabarar, Zarina ta yi nazarin babi biyu na littafin nan Menene Ainihi Littafi Mai Tsarki Yake Koyarwa? da yaranta, kafin su kaura zuwa wani wuri. A sabon wurin, ta sami zarafin koya wa yaranta game da Jehobah ba tare da an takura mata ba. A watan Oktoba 2016 ne yaran biyun suka yi baftisma, kuma sun gode wa mahaifiyarsu don basirar da ta yi amfani da ita ta koya musu gaskiya game da Allah.