Koma ka ga abin da ke ciki

Dole ne In Zama Mashaidin Jehobah Idan Suna Koya Mini Littafi Mai Tsarki?

Dole ne In Zama Mashaidin Jehobah Idan Suna Koya Mini Littafi Mai Tsarki?

 A’a, ba dole ba ne ka zama Mashaidi. Muna nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane da yawa kuma su ba Shaidun Jehobah ba ne. a Ainihin abin da yake sa mu yin nazari da mutane shi ne mu taimaka musu su san abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa. Amma kai ne za ka yi amfanin da abin da kake koya yadda ka ga dama. Mun san cewa in ya zo ga batun imani, mutum ne zai zabi abin da yake so.​—Joshua 24:15.

Zan iya yin amfani da nawa Littafi Mai Tsarki a lokacin Nazarin?

 E. Ko da yake muna amfani da New World Translation of the Holy Scriptures a Turanci domin yadda yake da saukin ganewa kuma muna iya ba wa mutane kyautarsa, hakan bai hana mu yin amfani da irin Littafi Mai Tsarki da mutumin yake da shi ba. Mutum zai iya koya gaskiya daga cikin kowane irin Littafi Mai Tsarki.

Me ya sa kuke yin nazarin Littafi Mai Tsarki da mutanen da ba za su so su zama Shaidun Jehobah?

  •   Asalin dalilin da ya sa Kiristoci suke koya wa mutane Kalmar Allah shi ne domin suna kaunar Jehobah. (Matta 22:​37, 38; 28:​19, 20) Mun san cewa gata mafi girma da mutane suke da shi shi ne su zama “abokan aiki na Allah,” suna koya ma wasu Kalmarsa.​—1 Korintiyawa 3:​6-9.

  •   Wani dalili kuma shi ne Kiristoci suna kaunar makwabtansu. (Matta 22:39) Muna jin dadin gaya wa mutane abubuwa masu ban mamaki da muka sani game da Allah.​​—Ayyukan Manzanni 20:35.

a Domin ka san abin da muka cim ma a shekara ta 2022, mun yi nazarin Littafi Mai Tsarki da mutane 5,666,996 a kowane wata kuma a wasu lokuta, mun yi hakan da mutane da yawa a lokaci daya. Duk da haka, mutane 145,552 ne kawai suka yarda su yi baftisma a matsayin Shaidun Jehobah a shekarar.