Koma ka ga abin da ke ciki

Hasumiyar Tsaro—Babu Wata Mujalla da ta Yi Kusa da Su

Hasumiyar Tsaro—Babu Wata Mujalla da ta Yi Kusa da Su

Ana rarraba Hasumiyar Tsaro fiye da kowace mujalla a duniya. Ana buga kowace fitar ta fiye da kofi miliyan 42. Awake! kuma na biyunta, ana buga kofi miliyan 41 a kowace fitar ta. Shaidun Jehobah ne suke buga mujallu biyun kuma ana rarraba su a ƙasashe 236.

Ta yaya za a iya gwada su da wasu littattafai? In ji The Association of Magazine Media, mujallar da ƙungiyar AARP ta Amirka take bugawa domin mutane ’yan shekara sama da 50. Ana rarraba mujallar sama da kofi miliyan 22.4. ADAC Motorwelt na Jamus tana da avirejin kusan kofi miliyan 14, da kuma (labaran) Gushi Hui na Sin da ake buga kofi miliyan 5.4.

Game da jaridun labarai da aka fi rarrabawa, Yomiuri Shimbun na Japan ne ke kan gaba. A kowane lokaci, ana buga fiye da kofi miliyan goma.

Game da fassara, an fi fassara Littattafan Shaidu. Ana fassara Hasumiyar Tsaro a harsuna fiye da 190, da kuma Awake! zuwa fiye da harsuna 80. Idan muka duba, ana buga Reader’s Digest a harsuna 21, ko da yake abin da ke ciki ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa.

Akasin sauran mujallu da aka ambata anan, Hasumiyar Tsaro da Awake! ba su da farashi, ana ba da tallafi ne ta hanyar gudummawar da aka ba da da son rai.

Manufar Hasumiyar Tsaro ita ce ta bayyana koyarwar Littafi Mai Tsarki—kuma musamman ma abin da Nassosi suka ce game da Mulkin Allah. An soma buga ta tun shekara ta 1879. Awake! tana bincika batutuwa galibi, irinsu halitta da kuma kimiyya, da niyyar ƙarfafa imani ga Mahalicci. Tana kuma nanata yadda Littafi Mai Tsarki yake da amfani a rayuwarmu.