Koma ka ga abin da ke ciki

An Baza Wani Irin Koli Mai Tamani a Kasar Botswana

An Baza Wani Irin Koli Mai Tamani a Kasar Botswana

Daga ranar 22 zuwa 28 ga watan Agusta, 2016, a Bostwana kasar da aka fi hakar lu’ulu’u a duniya, Shaidun Jehobah sun kawo abubuwa masu tamani da suka bambanta a kasuwar baza kolin da aka yi a kasar. A rumfarsu sun baza littattafan da ke bayyana Littafi Mai Tsarki da abin da ke nuna dandalin jw.org da kuma bidiyoyin da ke taimaka wa iyalai su kasance da farin ciki.

Iyaye da yaran da suka ziyarci rumfar sun ji dadin kallon bidiyoyin Ka Zama Abokin Jehobah, wanda yake koyar da yadda za a rika bin ka’idodin Littafi Mai Tsarki. Da yake irin wannan bidiyoyin ba su da yawa a yaren Setswana wato yaren da aka fi yi a kasar Botswana, mutane da yawa da suka zo suna ta tambayar inda za su sami wadannan bidiyoyin.

Bakin da suka zo daga kasashe dabam-dabam sun karbi littattafai 10,000, kari ga haka, mutane 120 suna so a soma yin nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Ban da haka ma, da yawa daga cikinsu sun ga yadda Shaidun Jehobah daga ikilisiyar Turanci da na yaren Setswana suke aiki tare da hadin kai kuma hakan ya burge su sosai.

Sa’ad da mutanen da suka tsara kasuwar baza kolin suka zo don ba da lambar yabo ga rumfunan, sun ba wa Shaidun Jehobah lamba na daya.