Koma ka ga abin da ke ciki

Dubbai Suna Ziyarar Ofishin Shaidun Jehobah da ke Amirka ta Tsakiya

Dubbai Suna Ziyarar Ofishin Shaidun Jehobah da ke Amirka ta Tsakiya

A shekara ta 2015, mutane kusan 175,000 ne suka je zagayar bude ido a ofishin Shaidun Jehobah da ke Meziko, wato mutane 670 a kowace rana da ake aiki ban da Asabar da Lahadi. Mutane da yawa da suka zo ziyarar sun zo da motar haya kuma sun yi tafiya kwanaki da yawa. Wasu sun yi watanni da yawa suna shirin yin wannan tafiyar.

“Shiri don Ziyarar Bethel”

Wasu sun yi sadaukarwa sosai don su ziyarci ofishin Shaidun Jehobah da ake kira Bethel. Alal misali, yawancin ‘yan’uwa a wata ikilisiya da ke jihar Veracruz a kasar Meziko ba su da kudin biyan tafiyar kilomita 550 da bas zuwa ofishin. Sai suka soma yin “Shiri don Ziyarar Bethel.” Kuma sun kafa wasu rukuni da za su rika dafa abinci suna sayarwa. Kari ga haka, sun sayar da tsofaffin robobi. Bayan watanni uku, sai suka samu isashen kudi na yin tafiyar.

Shin sun amfana don sadaukarwa da suka yi? Kwarai kuwa. Alal misali, wani matashi da ke ikilisiyar mai suna Lucio ya rubuto cewa: “Ziyarar da muka kai zuwa Bethel ta sa na dada kafa wasu makasudai, kuma yanzu na kara kwazo a ikilisiyarmu.” Ban da haka ma, Elizabeth ‘yar shekara 18 ta ce: “A Bethel na ga cewa wadanda suke bauta wa Jehobah suna kaunar juna sosai. Hakan ya sa na kara kwazo a bautar Allah, kuma na soma hidima ta cikakken lokaci.”

Dubbai ne Suke Zuwa

A wasu lokuta, dubban mutane ne suke zuwa don zagayar bude ido a rana. ‘Yan’uwa da suke aiki a Sashen Zagayar Bude Ido suna aiki tukuru don su marabce su da kyau. Lizzy ta ce: “Ina farin cikin ganin mutane da yawa suna zuwa ziyara. Ganin yadda bakin suke farin ciki da irin sadaukarwa da suka yi don su ziyarci ofishin nan yana karfafa ni sosai.”

’Yan’uwa da suke wasu hidimomi a Bethel ma suna kai mutane da yawa zagayar bude ido. Ko da yake yin hakan yana nufin karin aiki, suna farin cikin marabtar wadannan bakin. Juan ta ce: “Bayan na kai mutane zagaya, kuma na ga suna farin ciki, hakan yana sa ni farin ciki sosai.”

“Yara Suna Son Hoton”

Yara ma suna jin dadin ziyarar Bethel. Noriko, wadda take aiki a Sashen Kwamfuta ta ce: “Na tambayi yaran da suka zo ziyarar ko za su so su yi hidima a Bethel. Dukansu sun ce, ‘E!’ ” Wurin da yara suka fi so shi ne wurin da “Hoton Kaleb” yake. A wurin suna iya daukan hoto da babban zanen Kaleb da Safiya, da aka dauko daga jerin bidiyo na Ka Zama Abokin Jehobah. Noriko ta ce: “Yara suna son hoton sosai.”

Yara da yawa sun ce suna godiya don aikin da ake yi a Bethel. Alal misali, wani karamin yaro mai suna Henry daga Meziko ya tara kudi a cikin asusu don ya yi gudummawa da shi sa’ad da ya zo Bethel ziyara. Ya rubuta wasika da ya hada da gudummawar, ya ce: “Don Allah ku yi amfani da wannan kudin don ku kara wallafa littattafai. Muna godiya don kuna wa Jehobah aiki.”

Muna Gayyatarku Ku Zo

Shaidun Jehobah suna kai mutane zagayar bude ido a ofisoshinsu da kuma wuraren da suke buga littattafai a fadin duniya. Idan za ka so ka ziyarci wani ofishi, muna gayyatarka ka zo. Babu shakka mun tabbata za ka ji dadin ziyararka. Za ka samu karin bayani a kan yadda ake wannan zagayar bude ido a dandalinmu a karkashin GAME DA MU > OFISOSHI DA ZAGAYA.