Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 98

Nassosi Hurarre Ne Daga Allah

Nassosi Hurarre Ne Daga Allah

(2 Timotawus 3:​16, 17)

  1. 1. Kalmar Allah na taimaka,

    Tana sa mu ga haske.

    In muna bin umurninta,

    Za mu ceci rayukanmu.

  2. 2. Ya yi tanadin Kalmarsa,

    Don mu san umurninsa.

    Tana ƙarfafa mutane,

    Tana horar da mu sosai.

  3. 3. Kalmar Allah ta sa mu san,

    Cewa Yana da ƙauna.

    Karanta ta a koyaushe

    Zai sa mu riƙe aminci.

(Ka kuma duba Zab. 119:105; Mis. 4:13.)