Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 44

Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala

Addu’ar Wanda Ke Cikin Wahala

(Zabura 4:1)

  1. 1. Ya Allahna ina roƙo ka ji:

    “Addu’ata.”

    Matsaloli sun yi yawa;

    za su fi ƙarfina.

    Baƙin ciki da ƙunci

    suna sa ni in gaji.

    Ya Allah, ka taimake ni;

    don in yi nasara.

    (AMSHI)

    Taimake ni don in jimre.

    In na gaji, taimake ni.

    Ina roƙo don ƙuncina.

    Ya Allahna, ji roƙona.

  2. 2. Ina karanta Kalmarka

    lokacin damuwa

    Domin tana kwantar mini

    da hankali sosai.

    Bari ta sa na gaskata

    da alkawuranka.

    Domin in riƙa ƙaunar ka

    cikin rayuwata.

    (AMSHI)

    Taimake ni don in jimre.

    In na gaji, taimake ni.

    Ina roƙo don ƙuncina.

    Ya Allahna, ji roƙona.

(Ka kuma duba Zab. 42:6; 119:28; Rom. 8:26; 2 Kor. 4:16; 1 Yoh. 3:20.)