Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 139

Rayuwa a Cikin Aljanna

Rayuwa a Cikin Aljanna

(Ru’ya ta Yohanna 21:​1-5)

  1. 1. Ka ga kanka, ka gan ni ma,

    Ka gan mu duk a cikin aljanna.

    Yin rayuwa a aljanna

    Zai yi daɗi, kome zai yi kyau.

    Za a kawar da mugaye,

    Mulkin Jehobah zai dawwama.

    A lokacin da muke a aljanna

    Duk za mu yi murna

    muna rera yabo:

    (AMSHI)

    “Mun gode Allah don ayyukanka.

    Ɗanka Yesu ya gyara duniya.

    Muna godiya sosai don albarkarka.

    Muna rera waƙar yabo ga sunanka.”

  2. 2. Ka ga kanka, ka gan ni ma,

    Ka gan mu muna jin daɗi sosai.

    Babu kome a duniya

    Da zai sa mu riƙa jin tsoro.

    Alkawuran Maɗaukaki

    Duk sun cika yadda ya faɗa.

    Jehobah Uba, zai ta da matattu,

    Duk za mu rera yabo

    da murna sosai:

    (AMSHI)

    “Mun gode Allah don ayyukanka.

    Ɗanka Yesu ya gyara duniya.

    Muna godiya sosai don albarkarka.

    Muna rera waƙar yabo ga sunanka.”

(Ka kuma duba Zab. 37:​10, 11; Isha. 65:17; Yoh. 5:28; 2 Bit. 3:13.)