Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

WAƘA TA 13

Mu Rika Bin Misalin Yesu

Mu Rika Bin Misalin Yesu

(1 Bitrus 2:21)

  1. 1. Jehobah mai ƙauna,

    Ya albarkace mu,

    Ya aiko Yesu domin ya cece mu.

    Ɗansa Yesu Kristi,

    Ya zo duniyar nan,

    Don ya ɗaukaka Jehobah Allah.

  2. 2. Kalmar Jehobah ce,

    Ta taimaki Yesu.

    Ya zama mai hikima da basira.

    Ɗan Allah ya nuna,

    Shi bawan kirki ne,

    Yana jin daɗin yin nufin Allah.

  3. 3. Mu bi misalin da

    Ɗan Allah ya kafa

    Don ayyukanmu su yabi Jehobah.

    Mu riƙa bin gurbin

    Da Yesu ya kafa

    Domin mu more rai har abada.

(Ka kuma duba Yoh. 8:29; Afis. 5:2; Filib. 2:​5-7.)