Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

YADDA AKE AMFANI DA GUDUMMAWARKA

Taron Ikilisiya ta Hanyar Bidiyo

Taron Ikilisiya ta Hanyar Bidiyo

26 GA YUNI, 2020

 Hukumomi da yawa a duniya ba sa so mutane su rika yin kusa da juna da kuma taro saboda cutar coronavirus. Shaidun Jehobah sun kuduri niyyar bin wannan dokar, amma duk da haka, za su rika yin taro. Don haka, ikilisiyoyi suna yin amfani da manhajar yin taro ta hanyar bidiyo kamar wanda ake kira Zoom.

 Domin a rika yin taro a kai a kai da kuma a hanyar da ba za a saka ʼyan’uwa cikin hadari ba, Hukumar da Ke Kula da Ayyukanmu ta amince a yi amfani da gudummar da ake bayarwa don a bude asusu da dama a Zoom. Hakan ya taimaki wasu ikilisiyoyi da ba su da dala 15 zuwa 20 ko kuma sama da hakan don bude asusu a Zoom. A dā, ikilisiyoyin nan suna yin amfani da asusun Zoom da ba a biyan kudi kuma wannan asusun ba shi da tsaro sosai kuma mutane da yawa ba sa iya halartan taro. Dukan ikilisiyoyin da ke yin amfani da Zoom da ake biyan kudi suna amfana sosai domin yana da sauki kuma mutane da yawa za su iya halartan taro. A yanzu, ikilisiyoyi sama da 65,000 a kasashe fiye da 170 suna yin amfani da asusun.

 Ikilisiyar Kairagi a birnin Manado, Arewacin Sulawesi, Indonesiya ta soma yin amfani da asusun Zoom da kungiyarmu ta tanadar. Dan’uwa Hadi Santoso ya bayyana cewa: “Har ʼyan’uwa da ba su iya amfani da na’ura ba sosai suna jin dadin halartan taro domin ba sa bukatar su shiga taron, su kuma fita sau da yawa.”

 Wani dattijo mai suna Lester Jijón, Jr., a Ikilisiyar Guayacanes Oeste a Guayaquil, kasar Ecuador, ya ce: “Saboda rashin kudi, ba zai yiwu wasu ikilisiyoyi su biya kudin Zoom domin dukan ʼyan’uwa a ikilisiya su halarci taro ba. Amma domin wannan sabon shirin da aka yi, muna iya gayyatar mutane da yawa su halarci taron kyauta, ba tare da jin tsoro cewa abin zai yanke ba.”

 Wani dattijo mai suna Johnson Mwanza, a Ikilisiyar Ngwerere North a Lusaka, Zambiya, ya ce: “’Yan’uwa da yawa sun fadi sau da yawa cewa, ‘wannan shirin Zoom yana sa mu kusaci ’yan’uwanmu kuma mu ga cewa Jehobah yana kaunar mu kuma ya damu da mu.’”

 Kungiyarmu ta yi amfani da kudaden agaji don ta bude wannan asusun Zoom. Ana samun kudaden nan daga gudummawar da ake bayarwa don aiki na dukan duniya. Mutane da yawa suna shigan shafin donate.isa4310.com don su ba da gudummawa. Muna godiya don gudummawar da kuke bayarwa da dukan zuciyarku. Tana sa a tanadar da kayan agaji ga ʼyan’uwa a fadin duniya.​—2 Korintiyawa 8:14.