Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Zanen da Ke Wani Bango a Kasar Masar Ya Jitu da Wani Labari a Littafi Mai Tsarki

Zanen da Ke Wani Bango a Kasar Masar Ya Jitu da Wani Labari a Littafi Mai Tsarki

 Wannan zanen da ke bango mai-tsawon mita takwas yana kusa da kofar shiga wani haikali na allahn mutanen Masar mai suna Amun a Karnak. Masana sun ce wannan zanen da ke bangon yana nuni ne ga yawan yaki da Fir’auna Shishak ya ci a yankunan da ke arewa maso gabas a kasar Masar, har da Yahuda da kuma arewancin Isra’ila.

Zanen da ke bango a Karnak, hoton ya nuna bayin da aka daure

 Zanen ya nuna yadda Amun yake mika wa Shishak ko Sheshonk bayi fiye da 150. a Kowane bawa yana wakiltar gari ko mutanen da aka ci su da yaki. An rubuta sunan kowane gari a jikin kowane bawa. Har a yau, ana iya karanta wasu sunayen, kuma mutanen da suke karanta Littafi Mai Tsarki sun san wasu cikin sunayen nan sosai. Sunaye kamar su Beth-shean da Gibiyon da Magiddo da kuma Shunem.

 A Littafi Mai Tsarki, an ambata yadda sojojin Masar suka shiga kasar Yahuda. (1 Sarakuna 14:​25, 26) Littafi Mai Tsarki ya bayyana dalla- dalla yadda Shishak ya shiga kasar. Ya ce: “A shekara ta biyar ta mulkin Rehobowam, sai Sarki Shishak na Masar ya kawo yaki a Urushalima. Shishak ya zo da kekunan doki dubu ɗaya da ɗari biyu (1,200), da masu hawan doki dubu sittin (60,000), tare da sojojin da ba a iya kirgawa. . . . Ya kwace birane masu katanga na Yahuda, ya wuce har zuwa Urushalima.”​—2 Tarihi 12:​2-4.

 Ba zanen da ke bango a Karnak ne kawai ya tabbatar cewa Shishak ya shiga yankin Isra’ilawa ba. Wani rubutun da aka yi a kan gutsuren dutse da aka gano a wani garin da ake kira Magiddo yana dauke da sunan “Sheshonk.”

 Yadda Littafi Mai Tsarki ya ba da cikakkiyar bayani game da yadda Shishak ya ci kasar Yahuda da yaki, ya nuna yadda wadanda suka rubuta Littafi Mai Tsarki suke da aminci. Sun rubuta yadda aka ci kasarsu da yaki, ba su boye kome ba. Da kyar ake samun marubuta a zamanin dā da suke rubuta gaskiya kamar haka.

a Yadda aka rubuta “Shishak” a Littafi Mai Tsarki ya nuna yadda ake kiran sunan a Ibraniyanci.