Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Maremagnum/Corbis Documentary via Getty Images

KU ZAUNA A SHIRYE!

Daga Kasar Israꞌila ne Za A Soma Armageddon?​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

Daga Kasar Israꞌila ne Za A Soma Armageddon?​—Mene ne Littafi Mai Tsarki Ya Ce?

 Littafi Mai Tsarki bai ce Armageddon yaki ne da za a yi a wani bangaren duniya kawai ba. Amma ya ce yaki ne da za a yi a fadin duniya tsakanin gwamnatocin ꞌyan Adam da Allah.

  •   “Maganganun ne da suka fito daga aljanu . . . suna kuwa fita zuwa wurin dukan sarakunan duniya, domin su tattara su saboda yaki a babbar Ranar nan ta Allah Mai Iko Duka. . . . Suka tattara sarakunan nan wuri daya, a wurin da ake ce da shi Armageddon.”​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 16:​14, 16, New World Translation.

 An sami kalmar nan “Armageddon” ne daga kalmar Ibraniyancin nan Har Meghid·dohnʹ, wanda yake nufin “Dutsen Megiddo.” Megiddo wani birni ne a yankin Israꞌila ta dā. Don haka, wasu mutane suna ganin a kasar Israꞌila ne za a yi yakin Armageddon. Amma zai yi wuya a ce yankin Megiddo ko wani wuri a Gabas ta Tsakiya zai iya daukan “dukan sarakunan duniya” da rundunan su.

 An yi amfani da alamu wajen rubuta littafin Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna. (Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 1:1) Armageddon ba wani wuri ba ne a duniyar nan, amma wani yanayi ne da zai sa kasashe su taru don su yi gāba da Mulkin Allah.​—Ruꞌuyar da Aka Yi wa Yohanna 19:​11-16, 19-21.