Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Rashin Fahimta Karamar Matsala Ce?

Rashin Fahimta Karamar Matsala Ce?

Wata ƙaramar yarinya ta ga hayaƙi yana fitowa daga wani kamfani kuma yana ta ƙaruwa. Amma sai ta ɗauka cewa an yi kamfanin ne don ya riƙa sa hadari ya haɗu. Irin wannan rashin fahimta abin ban dariya ne. Amma, rashin fahimtar wasu abubuwa yana iya shafan rayuwarmu. Alal misali, rashin fahimtar bayanan da ke kwalbar magani yana iya jawo mummunan sakamako.

Rashin fahimtar abubuwa na ibada sun fi jawo mummunan sakamako. Alal misali, wasu mutane ba su fahimci koyarwar Yesu ba. (Yohanna 6:48-68) Amma maimakon su tsaya su fahimta sosai, sai suka yi banza da dukan abubuwan da Yesu ya koya musu. Wannan babbar hasara ce!

Shin kana karanta Littafi Mai Tsarki don ya ja-gorance ka? Idan haka ne, yana da kyau. Amma zai iya yiwu cewa ba za ka fahimci wasu abubuwan da ka karanta ba? Hakan na faruwa da mutane da yawa. Ka yi la’akari da misalai uku da ruwan dare gama gari ne.

  • Wasu mutane ba su fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce mu “ji tsoron Allah” ba. Sun ɗauka cewa yana nufin irin tsoron da muke wa abin da zai iya jawo mana lahani. (Mai-Wa’azi 12:13) Amma ba irin tsoron da Allah yake bukata a gare mu ba ke nan. Allah ya ce: “Kada ka ji tsoro; gama ina tare da kai: kada ka yi fargaba; gama ni ne Allahnka: ni ƙarfafa ka: ni taimake ka.” (Ishaya 41:10) Jin tsoron Allah yana nufin daraja shi da kuma girmama shi.

  • Shin za a ƙona duniya da wuta?

    Wasu mutane ba su fahimci abin da hurarren kalmomin nan suke nufi ba: “Kome da lokacinsa, . . . akwai lokacin haifuwa, da lokacin mutuwa.” Suna tunani cewa Allah ya riga ya ƙaddara lokacin da kowane ɗan Adam zai mutu. (Mai-Wa’azi 3:1, 2) Amma waɗannan ayoyin suna magana ne a kan abin da ke yawan faruwa da ‘yan Adam, wato suna haihuwa da kuma mutuwa. Kalmar Allah ta kuma nuna cewa zaɓin da muke yi zai iya shafanmu. Alal misali, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Tsoron Ubangiji yakan tsawonta kwanakin rai.” (Misalai 10:27; Zabura 90:10; Ishaya 55:3) A wace hanya? Alal misali, idan muna daraja Kalmar Allah, za mu nisanta kanmu daga munanan halaye kamar su buguwa da giya da kuma yin lalata.1 Korintiyawa 6:9, 10.

  • Wasu ba su fahimci abin da Littafi Mai Tsarki yake nufi sa’ad da ya ce an tanaje sammai da duniya “domin wuta” ba. Suna tsammani cewa hakan na nufin Allah zai halaka sama da kuma doron ƙasa. (2 Bitrus 3:7) Amma Allah ya yi alkawari cewa ba zai taɓa ƙyale a halaka doron ƙasa ba. Littafi Mai Tsarki ya ce Allah “ya kafa tussan duniya, domin kada ta jijjigu har abada.” (Zabura 104:5; Ishaya 45:18) Miyagun mutanen da ke duniya ne Allah zai halaka har abada kamar yadda wuta ke halaka abu. A zahiri, kalmar nan sama tana iya nufin gajimare ko sararin sama ko kuma wurin zaman Allah. Wannan saman ne ba za a taɓa halakawa ba.

ME YA SA WASU BA SA YAWAN FAHIMTAR LITTAFI MAI TSARKI?

Waɗannan misalai sun nuna cewa mutane suna yawan fahimtar wasu kalmomin Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba ta dace ba. Amma me ya sa Allah yake ƙyale hakan ya faru? Wasu suna iya tunanin cewa: ‘Da yake Allah ya fi kowa hikima da kuma sanin kome, ya kamata ya ba mu littafin da za mu fahimci kome da ke cikinsa. Amma me ya sa bai yi hakan ba?’ Ka yi la’akari da waɗannan dalilai uku da suka sa mutane ba sa fahimtar Littafi Mai Tsarki yadda ya dace.

  1. An rubuta Littafi Mai Tsarki ne don mutanen da suke da sauƙin kai kuma suke so su fahimci abin da ke ciki. Yesu ya yi wannan furucin ga Ubansa, Jehobah: “Ina gode maka, ya Uba, Ubangijin sama da ƙasa, da ka ɓoye wa masu-hikima da masu-fahimi waɗannan al’amura, ka bayyana su ga jarirai.” (Luka 10:21) An rubuta Littafi Mai Tsarki domin mutanen da suke da zuciya mai kyau su fahimce shi. Mutane “masu-hikima da masu-fahimi” suna yawan yin fahariya kuma ba sa iya fahimtar Littafi Mai Tsarki. Amma mutanen da ke fahimtar saƙon da ke cikin Kalmar Allah suna kamar “jarirai,” wato suna da sauƙin kai kuma suna so su koya. Babu shakka, an rubuta Littafi Mai Tsarki a hanyar da ta dace.

  2. An rubuta shi ne don mutanen da suke so Allah ya taimake su su fahimci saƙon da ke cikinsa. Yesu ya nuna cewa mutane za su bukaci taimako don su fahimci abin da ya koyar. Amma ta yaya za su sami wannan taimakon? Yesu ya ce: “Mai-taimako, wato ruhu mai-tsarki, wanda Uban zai aiko a cikin sunana, zai koya muku abubuwa duka.” (Yohanna 14:26) Saboda haka, Allah yana ba da ruhunsa mai tsarki, wato ikon da yake amfani da shi wajen cim ma nufinsa wajen taimaka wa mutane su fahimci abin da suka karanta a Littafi Mai Tsarki. Amma Allah ba ya ba da ruhunsa ga mutanen da ba sa dogara gare shi kuma irin waɗannan mutanen ba sa fahimtar saƙon da ke cikinsa. Ruhu mai tsarki yana kuma sa mutanen da suka fahimci Littafi Mai Tsarki sosai su taimaki waɗanda suke bukatar taimako.Ayyukan Manzanni 8:26-35.

  3. A lokacin da aka ƙayyade ne kaɗai mutane za su iya fahimtar wasu wurare a cikin Littafi Mai Tsarki. Alal misali, an ce annabi Daniyel ya rubuta wasu abubuwa da za su faru a nan gaba. Wani mala’ika ya ce masa: “Daniyel, ka kulle zantattukan, ka rufe littafin da hatimi, har kwanakin ƙarshe.” A cikin shekaru da yawa da suka shige, mutane da dama sun karanta littafin Daniyel amma ba su fahimci saƙon da ke cikinsa ba. Har Daniyel da kansa da ya rubuta littafin bai fahimci wasu abubuwan da ya rubuta ba. Shi ya sa ya ce: “Na ji, amma ban gane ba.” Daga baya, mutane za su fahimci annabcin da Daniyel ya rubuta, amma sai a lokacin da Allah ya ƙayyade. Mala’ikan ya ce: “Yi tafiyarka, ya Daniyel, gama an kulle zantattukan, an hatimce su har kwanakin ƙarshe.” Su waye ne za su fahimci saƙon? “Daga cikin miyagu kuma babu mai-fahimtawa; amma waɗanda suke da hikima za su gane.” (Daniyel 12:4, 8-10) Hakan ya nuna cewa Allah ba ya bayyana ma’anar wasu wurare a cikin Littafi Mai Tsarki sai daidai lokacin da ya ƙayyade.

Shin Shaidun Jehobah sun taɓa fahimtar Littafi Mai Tsarki a hanyar da ba ta dace ba domin lokacin da aka ƙayyade bai yi ba tukun? Ƙwarai kuwa. Amma idan lokacin da Allah yake so mu fahimci wani batu ya kai, Shaidun Jehobah suna yin gyara ga yadda suka fahimci batun. Sun yi imani cewa yin hakan yana sa su yi koyi da manzannin Yesu domin sun daidaita ra’ayinsu a duk lokacin da Yesu ya yi musu gyara.Ayyukan Manzanni 1:6, 7.

Kuskuren da ƙaramar yarinyar da muka ambata ɗazun ta yi ba mai tsanani ba ne. Amma abin da Littafi Mai Tsarki yake koyarwa yana da muhimmanci sosai. Bai kamata kowa ya yi ƙoƙarin fahimtar saƙon da ke cikinsa ta wajen karanta littafin shi kaɗai ba. Saboda haka, zai dace ka nemi taimako don ka fahimci abin da kake karantawa. Ka nemi mutane masu sauƙin kai, mutanen da ke dangana ga ruhu mai tsarki don su fahimci saƙon. Da kuma mutanen da suka yi imani cewa muna rayuwa ne a lokacin da Allah yake so mu fahimci Littafi Mai Tsarki sosai. Kada ka yi jinkirin tattaunawa da Shaidun Jehobah ko kuma ka karanta bayanan da suka yi cikin dandalin jw.org. Littafi Mai Tsarki ya ce: ‘Idan ka nace bin ganewa za ka ruski sanin Allah.’Misalai 2:3-5.