Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

ABIN DA KE SHAFIN FARKO | ZAI YIWU A SAKE RAYUWA—BAYAN MUTUWA?

Matattu Suna da Bege Kuwa?

Matattu Suna da Bege Kuwa?

Shin matattu za su sake rayuwa kuwa?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: ‘Sa’a tana zuwa, inda dukan waɗanda suna cikin kabarbaru za su ji muryar [Yesu], su fito kuma.”Yohanna 5:28, 29.

Yesu ya yi annabci a kan lokacin da za a ta da dukan mutanen da suke cikin Kabari sa’ad da ya soma sarauta. Fernando da aka ambata a talifi na farko ya ce: “Na yi mamaki sosai a lokacin da na fara karanta littafin Yohanna 5:28, 29. Hakan ya sa na kasance da bege sosai kuma na soma yin tunani game da nan gaba da gaba gaɗi.”

A zamanin dā, Ayuba mai aminci ya sa rai cewa Allah zai ta da shi idan ya mutu. Ayuba ya yi wannan tambayar: “Idan mutum ya mutu za ya sake rayuwa?” Sai ya amsa da gaba gaɗi: “Dukan kwanakin yaƙina [lokacin da nake kabari] sai in jira, har a karɓe ni in huta. Za ka yi kira, ni ma in amsa maka.”Ayuba 14:14, 15.

Tashin Li’azaru daga mutuwa ya sa mun kasance da bege

Tashin matattu ba sabon abu ba ne ga Martha, ’yar’uwar Li’azaru. Bayan Li’azaru ya mutu, Yesu ya ce mata: “Ɗan’uwanki zai tashi kuma.” Martha ta ce masa: “Na sani za ya tashi kuma a cikin tashin matattu a kan rana ta ƙarshe.” Sai Yesu ya ce mata: “Ni ne tashin matattu, ni ne rai: wanda ya ba da gaskiya gare ni, ko ya mutu, zai rayu.” (Yohanna 11:23-25) Bayan haka, sai Yesu ya ta da Li’azaru daga mutuwa! Wannan labarin soma taɓi ne na abin da zai faru a nan gaba. Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance idan an ta da matattu a dukan duniya!

Shin za a ta da wasu zuwa sama ne?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Kalmar Allah ta nuna cewa tashin Yesu da aka yi daga mutuwa ya bambanta da guda takwas da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki. An ta da waɗannan mutane takwas a duniya. Amma ga abin da nassi ya ce game da na Yesu: “Yesu Kristi; shi wanda ke ga hannun dama na Allah, ya rigaya ya hau sama.” (1 Bitrus 3:21, 22) Ban da Yesu, shin da akwai wasu kuma da za a ta da zuwa sama? Yesu ya ce wa manzanninsa: “In kuwa na je na shirya muku wuri, sai in dawo in kai ku wurina, domin inda nake, ku ma ku zama kuna can.”Yohanna 14:3, Littafi Mai Tsarki.

Kristi ya je sama kuma ya yi shirye-shirye don zuwan wasu cikin almajiransa. Adadin mutane 144,000 ne za su je sama. (Ru’ya ta Yohanna 14:1, 3) Amma mene ne waɗannan mabiyan Yesu za su yi a sama?

Za su yi aiki tuƙuru! Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai-albarka kuma mai-tsarki ne shi wanda yake da rabonsa cikin tashi na fari: mutuwa ta biyu ba ta da iko bisansu; amma za su zama firistoci na Allah da na Kristi, za su yi mulki kuma tare da shi shekara dubu.” (Ru’ya ta Yohanna 20:6) Mutanen da za a ta da zuwa sama za su zama sarakuna da kuma firistoci tare da Kristi kuma za su yi sarauta bisa duniya.

Su waye za a tayar daga baya?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: An rubuta wannan furucin manzo Bulus cikin Nassosi: “Ina da bege ga Allah, abin da waɗannan da kansu kuma suna sauraronsa, za a yi tashin matattu, na masu adalci da na marasa adalci.”Ayyukan Manzanni 24:15.

Kalmar Allah ta tabbatar mana cewa biliyoyin mutanen da suka mutu za su sake rayuwa

Su waye ne “masu adalci” da Bulus ya ambata? Ga wani misali. Daniyel mutumi ne mai adalci kuma sa’ad da ya kusan mutuwa, an gaya masa cewa: Za “ka huta, a ƙarshen kwanaki za ka tashi ka karɓi naka rabo.” (Daniyel 12:13, LMT) A ina ne za a ta da Daniyel daga mutuwa? “Masu-adalci za su gāji ƙasan, su zauna a cikinta har abada.” (Zabura 37:29) Kuma Yesu ya yi wannan annabcin: “Masu-albarka ne masu-tawali’u: gama su za su gāji duniya.” (Matta 5:5) Za a ta da Daniyel da kuma wasu amintattun maza da mata don su sake rayuwa a duniya har abada.

Su waye ne “marasa adalci” da Bulus ya ambata? Su biliyoyin mutane ne da suka mutu, da yawa cikinsu ba su sami zarafin fahimta da kuma aikata gaskiyar da ke cikin Littafi Mai Tsarki ba. Bayan sun tashi daga mutuwa, za su sami zarafin sanin Jehobah * da kuma Yesu. (Yohanna 17:3) Dukan mutanen da suka yanke shawarar bauta wa Allah za su yi tsawon rayuwa kamar Jehobah, wato za su rayu har abada.

Dukan mutanen da suke bauta wa Allah za su yi rayuwa har abada cikin ƙoshin lafiya da kuma farin ciki

Yaya rayuwa za ta kasance a duniya?

ABIN DA LITTAFI MAI TSARKI YA CE: Allah “zai share dukan hawaye kuma daga idanunsu: mutuwa kuwa ba za ta ƙara kasancewa ba; ba kuwa za a ƙara yin baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) “Za su gina gidaje, kuma za su zauna a ciki; su yi gonakin anab kuma, su ci amfaninsu.”Ishaya 65:21.

Ka yi tunanin yadda rayuwa za ta kasance sa’ad da kake cikin irin wannan yanayin tare da mutanen da aka tayar daga mutuwa! Amma akwai wata tambaya da ba a amsa ba tukun, Ta yaya za ka kasance da tabbaci cewa za a ta da matattu?

^ sakin layi na 15 Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Jehobah shi ne sunan Allah.