Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

“Ka Kara Mana Bangaskiya”

“Ka Kara Mana Bangaskiya”

“Ka taimake ni in kasance da bangaskiya!”—MAR. 9:24, New World Translation.

WAƘOƘI: 81, 135

1. Ta yaya bangaskiya take da muhimmanci? (Ka duba hoton da ke shafin nan.)

KA TAƁA tambayar kanka ‘Shin Jehobah zai so ya ceci ni a lokacin ƙunci mai girma kuma ya sa in shiga cikin sabuwar duniya?’ Hakika, samun wannan ceton ya ƙunshi abubuwa da yawa, amma mafi muhimmanci shi ne abin da manzo Bulus ya ce: “Ba ya kuwa yiwuwa a gamshe shi [Allah] ba sai tare da bangaskiya.” (Ibran. 11:6) Hakan zai iya kasancewa da sauƙi, amma gaskiyar ita ce “ba duka ke da imani ba.” (2 Tas. 3:2) Waɗannan ayoyin sun taimaka mana mu fahimci cewa yana da muhimmanci mu kasance da bangaskiya sosai.

2, 3. (a) Ta yaya Bitrus ya koya mana cewa bangaskiya tana da muhimmanci? (b) Waɗanne tambayoyi ne za mu tattauna yanzu?

2 Manzo Bitrus ya nuna cewa bangaskiya tana da muhimmanci sosai sa’ad da ya yi magana game da tabbatacciyar bangaskiya wadda “ta kai zuwa yabo da daraja da girma a kan bayyanuwar Yesu Kristi.” (Karanta 1 Bitrus 1:7.) Tun da yake ƙunci mai girma yana nan tafe, muna son mu tabbata cewa mun kasance da bangaskiya da za ta sa mu zama cikin waɗanda Yesu Kristi zai albarkace su sa’ad da ya bayyana a matsayinsa na Sarki mai ɗaukaka. Hakika, muna so mu zama “cikin waɗanda suke da bangaskiya zuwa ceton rai.” (Ibran. 10:39) Saboda haka, bari mu yi roƙo kamar wani mutumin da ya ce: “Ka taimake ni in kasance da bangaskiya.” (Mar. 9:24, NW) Ko kuma mu ce kamar manzannin Yesu: “Ka ƙara mana bangaskiya.”—Luk. 17:5.

3 A wannan talifin za mu tattauna wasu tambayoyi game da bangaskiya. Ta yaya za mu ƙarfafa bangaskiyarmu? Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya? Wane tabbaci muke da shi cewa idan muka roƙi Allah, zai ƙara mana bangaskiya?

ALLAH YANA SON MU ƘARFAFA BANGASKIYARMU

4. Waɗanne misalai ne za su sa mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

4 Za mu iya koyan darussa daga mutane da yawa da suka kafa misali mai kyau da ke cikin Littafi mai Tsarki, tun da yake ‘iyakar abin da aka rubuta a dā an rubuta su domin koyarwarmu’ ne. (Rom. 15:4) Karanta labaran mutane kamar Ibrahim da Saratu da Ishaƙu da Yakubu da Musa da Rahab da Gidiyon da Barak da dai sauransu zai sa mu bincika kanmu ko muna da bangaskiya sosai. (Ibran. 11:32-35) Ƙari ga haka, za mu yi iya ƙoƙarinmu mu ƙarfafa bangaskiyarmu idan muka karanta labaran ’yan’uwa maza da mata masu bangaskiya sosai a zamaninmu. *

5. Ta yaya Iliya ya nuna cewa ya gaskata sosai da Jehobah, kuma wace tambaya ce ya kamata mu yi wa kanmu?

5 Wani misali da ke cikin Littafi Mai Tsarki shi ne na annabi Iliya. Ka yi tunani a kan wasu abubuwan da suka faru da suka nuna cewa ya dogara sosai ga Jehobah. Sa’ad da Iliya ya gaya wa Sarki Ahab cewa Jehobah zai hana ruwan sama a ƙasar, ya yi hakan da gaba gaɗi kuma ya ce: “Na rantse da Ubangiji, Allah . . . ba za a yi raɓa ko ruwan sama . . . sai da faɗata.” (1 Sar. 17:1) Iliya ya gaskata cewa Jehobah zai biya bukatunsa da na wasu a lokacin fāri. (1 Sar. 17:4, 5, 13, 14) Ya kasance da aminci cewa Jehobah zai ta da wani yaro daga mutuwa. (1 Sar. 17:21) Bai yi shakka ba cewa Jehobah zai aiko da wuta ta cinye hadayarsa a Dutsen Karmel. (1 Sar. 18:24, 37) Sa’ad da lokaci ya yi da Jehobah zai kawo ƙarshen farin, kafin a ga alama cewa za a yi ruwa, Iliya ya gaya wa Ahab: “Ka hau, ka ci, ka sha; gama da motsin ruwan sama mai-yawa.” (1 Sar. 18:41) Karanta waɗannan labaran zai sa mu bincika kanmu ko muna da bangaskiya sosai.

MENE NE ZA MU YI DON MU ƘARFAFA BANGASKIYARMU?

6. Mene ne muke bukatar Jehobah ya ba mu don mu ƙarfafa bangaskiyarmu?

6 Tun da yake ba za mu iya ƙarfafa bangaskiyarmu da kanmu ba, muna bukatar mu roƙi Allah ya ba mu ruhunsa mai tsarki. Me ya sa? Domin bangaskiya tana cikin halayen da ruhu mai tsarki yake bayarwa. (Gal. 5:22) Saboda haka, ya dace mu bi shawarar Yesu kuma mu roƙi Allah ya ci gaba da ba mu ruhu mai tsarki domin Yesu ya tabbatar mana cewa Uban ‘za ya ba da Ruhu Mai-tsarki ga waɗanda suke roƙonsa.’—Luk. 11:13.

7. Ka kwatanta yadda za mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu.

7 Muddin mun ba da gaskiya ga Allah, wajibi ne mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu. Muna iya gwada bangaskiya da wuta. Idan muka cinna wuta, zai riƙa ci sosai. Idan aka ƙyale wutar, zai zama garwashi, daga baya ya zama toka. Amma, idan kana saka itace a kai a kai, wutar ba zai mutu ba. Hakazalika, za mu ci gaba da kasancewa da bangaskiya idan muka ci gaba da karanta da kuma nazarin Kalmar Allah a kai a kai. Hakan zai sa mu ƙaunaci Jehobah sosai da kuma kalmarsa. Ta yin hakan za mu ƙarfafa bangaskiyarmu sosai.

8. Mene ne zai taimaka mana mu ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarmu?

8 Mene ne kuma za ka ƙara yi don ka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarka? Ka ci gaba da koyan abubuwa da za su ƙarfafa bangaskiyarka bayan ka yi baftisma. (Ibran. 6:1, 2) Alal misali, za ka iya ci gaba da nazarin annabce-annabcen Littafi Mai Tsarki da suka cika domin za su taimaka maka ka ci gaba da ƙarfafa bangaskiyarka. Ƙari ga haka, za ka iya yin amfani da Kalmar Allah don ka bincika kanka ko kana da bangaskiya sosai.—Karanta Yaƙub 1:25; 2:24, 26.

9, 10. Ta yaya muke ƙarfafa bangaskiyarmu ta: (a) yin tarayya da abokan kirki? (b) halartan taron ikilisiya? (c) yin wa’azin bishara?

9 Manzo Bulus ya gaya wa ’yan’uwansa Kiristoci cewa za su iya ‘ƙarfafa juna ta bangaskiyarsu.’ (Rom. 1:12, Littafi Mai Tsarki) Yayin da muke cuɗanya da ’yan’uwa, za mu iya ƙarfafa bangaskiyar juna musamman a lokacin da muke tare da waɗanda sun riga sun ƙarfafa bangaskiyarsu sosai. (Yaƙ. 1:3) Tarayya da abokan banza tana haddasa rashin bangaskiya, amma yin cuɗanya da abokan kirki zai ƙarfafa bangaskiyarmu sosai. (1 Kor. 15:33) Shi ya sa aka ba mu shawara cewa kada mu riƙa “fasa” taro, amma mu ci gaba da “gargaɗar da juna.” (Karanta Ibraniyawa 10:24, 25.) Wani dalili kuma shi ne cewa abubuwan da muke koya a taron ikilisiya suna ƙarfafa bangaskiyarmu. Hakan ya jitu da abin da Bulus ya faɗa: “Bangaskiya fa daga wurin ji ne.” (Rom. 10:17) Saboda haka, ka tambayi kanka, Shin ina cuɗanya da ’yan’uwa sa’ad da na halarci taro?

10 Idan muna wa’azi da kuma koya wa wasu Littafi Mai Tsarki, hakan zai ƙarfafa bangaskiyarmu. Kamar Kiristoci na farko, mun ba da gaskiya sosai ga Jehobah kuma muna magana gabanmu gaɗi a duk yanayin da muka samu kanmu.—A. M. 4:17-20; 13:46.

11. Me ya sa Kaleb da Joshua suka kasance da bangaskiya sosai, kuma ta yaya za mu yi koyi da su?

11 Muna ƙarfafa bangaskiyarmu ga Jehobah sa’ad da muka ga yadda yake taimaka mana da kuma yadda yake amsa addu’o’inmu. Abin da ya faru da Kaleb da Joshua ke nan. Sun dogara ga Jehobah sa’ad da suka je leƙen asirin Ƙasar Alkawari. Amma, da shigewar lokaci sun kasance da bangaskiya sosai yayin da suka shaida yadda Jehobah ya taimaka musu. Shi ya sa Joshua ya gaya wa Isra’ilawa cewa: “Babu wani abu ɗaya ya sare daga cikin dukan alherai waɗanda Ubangiji Allahnku ya ambace su a kanku.” Daga baya ya daɗa cewa: “Ku ji tsoron Ubangiji, ku bauta masa cikin sahihanci da cikin gaskiya . . . Da ni da gidana, Ubangiji za mu bauta wa.” (Josh. 23:14; 24:14, 15) Idan muka dogara ga Jehobah kuma muka lura da yadda yake taimaka mana, za mu ƙarfafa bangaskiyarmu sosai.—Zab. 34:8.

YADDA ZA MU NUNA BANGASKIYARMU

12. Mene ne Yaƙub ya nuna cewa yana da muhimmanci idan za mu kasance da bangaskiya?

12 Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya sosai? Almajiri Yaƙub ya amsa wannan tambayar ta wurin cewa: “Ni kuwa ta wurin ayyukana in nuna maka bangaskiyata.” (Yaƙ. 2:18) Abubuwan da muke yi za su nuna cewa muna da bangaskiya sosai. Bari mu bincika wasu misalai.

Waɗanda suka kasance da ƙwazo a yin wa’azin bishara sun nuna cewa suna da bangaskiya sosai (Ka duba sakin layi na 13)

13. Ta yaya yin wa’azi a hanyoyi dabam-dabam ya nuna cewa muna da bangaskiya?

13 Yin wa’azin bishara, hanya ce mafi kyau da za mu nuna cewa muna da bangaskiya sosai. Me ya sa? Domin sa’ad da muke wa’azi, muna nuna mun gaskata cewa ƙarshen ya kusa kuma ba zai “yi jinkiri ba.” (Hab. 2:3) Hanya ɗaya da za mu san ko muna da bangaskiya sosai ita ce ta wurin bincika ko muna a shirye mu yi wa’azi da ƙwazo. Shin muna yin iya ƙoƙarinmu a yin wa’azi da ƙwazo? Shin muna neman sababin hanyoyi na yin wa’azi kuwa? (2 Kor. 13:5) Hakika, yin wa’azin bishara ga mutane don su sami ceto hanya ɗaya ce mai muhimmanci da za mu nuna cewa muna da bangaskiya sosai.—Karanta Romawa 10:10.

14, 15. (a) Ta yaya za mu nuna cewa muna da bangaskiya a rayuwarmu ta yau da kullum? (b) Ka bayyana yadda wasu suka nuna cewa sun dogara ga Jehobah.

14 Sa’ad da muka jure da ƙalubale na yau da kullum, za mu kuma nuna cewa mun dogara ga Jehobah sosai. Muna da tabbaci cewa Jehobah da Ɗansa za su “taimake mu a kan kari” a lokacin da muke rashin lafiya ko sanyin gwiwa ko fama da talauci ko kuma wasu matsaloli. (Ibran. 4:16, LMT) Sa’ad da muka roƙi Jehobah ya taimake mu, muna dogara gare shi. Yesu ya ce muna iya yin addu’a don Jehobah ya biya bukatunmu, kuma hakan ya haɗa da “abincin yini.” (Luk. 11:3) Labaran Littafi Mai Tsarki sun nuna cewa Jehobah zai iya ba mu kome da muke bukata. Alal misali, a lokacin da ake fāri a ƙasar Isra’ila, Jehobah ya ba Iliya abinci da ruwa ta wajen aika ‘hankaki kuwa su kawo masa gurasa da nama da safe, gurasa da nama kuwa da yamma: ya kuwa sha daga cikin rafin.’ (1 Sar. 17:3-6) Muna da bangaskiya cewa Jehobah zai iya biyan bukatunmu.

Muna nuna bangaskiya idan muna yin iya ƙoƙarinmu duk da ƙalubalen da muke fuskanta (Ka duba sakin layi na 14)

15 Mun tabbata cewa bin ƙa’idodin Littafi Mai Tsarki zai taimaka mana mu ciyar da iyalinmu. Rebecca, wata ’yar’uwa a Asiya ta shaida hakan a iyalinta. Sun bi ƙa’idar da ke Matta 6:33 da Misalai 10:4, wato sun saka ibadarsu ga Jehobah kan gaba a rayuwarsu kuma suna aiki da ƙwazo. Rebecca ta ce a wani lokaci mijinta ya ga cewa aikinsa zai ɓata dangantakarsu da Jehobah, sai ya bar aikin. Amma suna da yara huɗu da za su kula da su. Rebecca ta ci gaba da cewa: “Muka soma sayar da abinci, kuma mun yi shekara da yawa muna wannan sana’ar, mun shaida cewa Jehobah bai yi watsi da mu ba. Ba mu taɓa kwana da yunwa ba.” Shin ka gaskata cewa Littafi Mai Tsarki yana ɗauke da ja-gora mafi amfani a yau?

16. Mene ne zai faru idan muka dogara ga Allah?

16 Ya kamata mu kasance da tabbaci cewa idan muka bi ja-gorar Allah, zai taimaka mana. Sa’ad da Bulus yake ƙaulin Habakkuk, ya ce: “Mai-adalci ta wurin bangaskiya zai rayu.” (Gal. 3:11; Hab. 2:4) Saboda haka, yana da muhimmanci mu ba da gaskiya ga Mai taimakonmu da gaske. Bulus ya tuna mana cewa Allah ne “wanda yake da iko shi aikata ƙwarai da gaske gaba da dukan abin da muke roƙo ko tsammani, bisa ga ikon da ke aikawa a cikinmu.” (Afis. 3:20) Bayin Jehobah suna iya ƙoƙarinsu don su yi nufin Allah, amma suna dogara ga Jehobah don sun san cewa suna da kasawa. Babu shakka muna godiya cewa Allah yana yi mana albarka saboda ƙoƙarin da muke yi.

AN AMSA ADDU’ARSU GAME DA BANGASKIYA

17. (a) Ta yaya aka amsa roƙon manzannin? (b) Me ya sa muke da tabbaci cewa Allah zai amsa roƙonmu na ƙarin bangaskiya?

17 Abin da muka tattauna a wannan talifin zai iya sa mu soma tunani cewa muna bukatar bangaskiya kamar manzannin Yesu da suka gaya masa cewa: “Ka ƙara mana bangaskiya.” (Luk. 17:5) An amsa roƙonsu, musamman ma a ranar Fentakos ta shekara ta 33, sa’ad da aka ba su ruhu mai tsarki kuma suka ƙara fahimta nufin Allah, kuma hakan ya ƙarfafa bangaskiyarsu. A sakamako, suka soma yin wa’azi bishara sosai a lokacin. (Kol. 1:23) Hakazalika, idan muka roƙi Allah ya ƙara mana bangaskiya, zai amsa addu’armu. Littafi Mai Tsarki ya tabbatar mana cewa za mu iya yin haka sa’ad da “mun roƙi kome daidai da nufinsa.”—1 Yoh. 5:14.

18. Ta yaya Jehobah yake albarkar waɗanda suka ba da gaskiya?

18 Hakika, idan muka dogara ga Jehobah, za mu sa shi farin ciki. Jehobah zai amsa roƙonmu na ƙarin bangaskiya. Ƙari ga haka, za mu kasance da bangaskiya sosai, kuma za mu zama waɗanda suka “cancanta ga Mulkin Allah.”—2 Tas. 1:3, 5.

^ sakin layi na 4 Don ka ga wasu misalai, ka duba tarihin Lillian Gobitas Klose (Awake! na 22 ga Yuli, 1993), Feliks Borys (Awake! na 22 ga Fabrairu, 1994), and Josephine Elias (Awake! na Satumba 2009).