Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Ta Yaya Za A Kawo Karshen Mutuwa?

Ta Yaya Za A Kawo Karshen Mutuwa?

KO DA yake rashin biyayyar da iyayenmu na fari suka yi ya sa mun zama ajizai kuma muna mutuwa, Allah bai fasa cika nufinsa na sa ’yan Adam su rayu har abada ba. A cikin Littafi Mai Tsarki, Allah ya ci gaba da tabbatar mana cewa bai canja nufinsa ba.

  • “Masu adalci za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.”​Zabura 37:29.

  • “Ubangiji Yahweh zai hallaka mutuwa har abada! Zai kuma share hawaye daga dukan fuskoki.”​Ishaya 25:8.

  • “Abokiyar gāba ta ƙarshe da za a kawar, ita ce mutuwa.”​1 Korintiyawa 15:26.

  • “Babu sauran mutuwa, ko baƙin ciki, ko kuka, ko azaba.”​Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 21:4.

Ta yaya Allah zai hallaka mutuwa? Littafi Mai Tsarki ya ce “masu adalci za su . . . zauna . . . har abada.” Amma ya kuma ce “babu mutum mai adalci a duniyar nan mai aikata abin da yake daidai a kowane lokaci.” (Mai-Wa’azi 7:20) Kana ganin Allah zai ƙyale mutane masu zunubi su ci gaba da rayuwa har abada ba tare da sun bi ƙa’idodinsa ba? Ko kaɗan! Allah zai cika abin da ya faɗa don “ba ya ƙarya.” (Titus 1:2) To, mene ne Allah zai yi da zai sa mutane su ji daɗin rayuwa har abada?

ALLAH “ZAI HALLAKA MUTUWA HAR ABADA.”​—ISHAYA 25:8

FANSA ZA TA KAWO ƘARSHEN MUTUWA

Jehobah ya shirya yadda zai kuɓutar da mu daga mutuwa, ta wajen ba da fansa. Idan Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmar nan fansa, yana nufin wani abu ne mai daraja da ake bayarwa don a saki mutum ko a biya hasarar da ya jawo bisa ga doka. Tun da dukanmu masu zunubi ne, kuma sakamakon zunubi shi ne mutuwa, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Hakika, babu mutum a cikinsu da zai iya fanshi wani, ko ya iya biya Allah kuɗi domin kansa. Gama kuɗin fansar ran mutum ya fi gaban misali, duk abin da mutumin zai iya biya, sam ba zai isa ba.”​—Zabura 49:​7, 8.

Sa’ad da mutum ya mutu, ya biya alhakin zunubinsa ne; ba zai iya ceton kansa daga ajizanci ba, balle ya biya ma wani alhakin zunubinsa don ya kuɓutar da shi daga mutuwa ba. (Romawa 6:7) Muna bukatar wani da bai taɓa yin zunubi ba ya ba da ransa, don zunubanmu.​—Ibraniyawa 10:​1-4.

Abin da Allah ya yi ke nan. Ya aiko da Ɗansa, Yesu, daga sama zuwa duniya kuma aka haife shi ba tare da wani aibi ba. (1 Bitrus 2:22) Yesu ya ce ya zo ya “ba da ransa domin ceton mutane da yawa.” (Markus 10:45) Ya zo ne don ya fanshe mu daga zunubi kuma ya kawo ƙarshen mutuwa.​—Yohanna 3:16.

A YAUSHE NE MUTANE ZA SU DAINA MUTUWA?

Muna rayuwa ne “a kwanakin ƙarshe” lokacin da “za a sha wahala sosai” kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya annabta. Irin matsalolin da muke fuskanta a yau sun nuna cewa muna “kwanakin ƙarshe.” (2 Timoti 3:1) Kwanakin nan za su ƙare a “ranar da za a yi wa marasa halin Allah hukunci, a hallaka su.” (2 Bitrus 3:​3, 7) Amma mutanen da suke ƙaunar Allah za su tsira kuma za su sami ladan “rai na har abada.”​—Matiyu 25:46.

Yesu ya zo ya “ba da ransa domin ceton mutane da yawa.”​—Markus 10:45

Miliyoyin mutane da za a ta da su daga mutuwa za su sami damar yin rayuwa har abada. Da Yesu yake duniya, ya ta da wani mutum daga mutuwa a lokacin da ya kai ziyara birnin Nayin. Mutumin da ya rasu ɗan wata gwauruwa ce, tilo. Yesu “ya ji tausayinta” kuma ya ta da ɗanta daga mutuwa. (Luka 7:​11-15) Manzo Bulus ya rubuta cewa: “Ina sa zuciya ga Allah, . . . cewa, za a tā da matattu, masu adalci da marasa adalci duka.” Wannan alkawarin ya nuna cewa Allah yana ƙaunar ’yan Adam.​—Ayyukan Manzanni 24:15.

Biliyoyin mutane za su iya sa ran yin rayuwa har abada. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu adalci za su gāji ƙasar, su zauna a ciki har abada.” (Zabura 37:29) A lokacin ne za su ga cikar kalmomin da manzo Bulus ya rubuta wajen shekara 2000 da suka shige, cewa: “Ke, mutuwa, ina nasararki? Ke, mutuwa, ina dafinki?” (1 Korintiyawa 15:55) Za su yi farin ciki sosai domin a lokacin, ba za a sake mutuwa ba!