Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Sayar da bayi tsakanin Afirka da kuma Amirka babbar sana’a ce sosai

Samun ‘Yanci Daga Bauta—A Zamanin Dā da Kuma Yanzu

Samun ‘Yanci Daga Bauta—A Zamanin Dā da Kuma Yanzu

An kai wata mai suna Blessing * ƙasar Turai kuma an yi mata alkawari cewa za a samo mata aikin gyarar suma. Maimakon haka, an tilasta mata ta shiga aikin karuwanci bayan an yi kwana goma ana dūkan ta da kuma yi mata barazana cewa za a kashe iyayenta idan ba ta yarda ba.

Hoton da ya nuna bayin da aka kama a ƙasar Masar ta dā

A kowane dare, Blessing tana bukatar ta sami Euro 200 zuwa 300 don ta iya biyan bashin sama da Euro 40,000 da uwar gidanta take bin ta. * Blessing ta ce, “Na yi tunanin guduwa amma ina jin tsoron abin da za su yi wa iyayena idan na yi hakan. Ina cikin tsaka mai wuya.” Labarinta ya yi kama da na mutane fiye da miliyan huɗu da suke karuwanci a ƙasar waje.

Wajen shekara 4,000 da suka wuce, ‘yan’uwan wani matashi mai suna Yusufu sun sayar da shi ga Masarawa kuma ya zama bawa a gidan wani attajiri. Da farko, ba a ci zalin Yusufu kamar yadda aka yi wa Blessing ba. Amma da ya ƙi kwana da matar ubangijinsa, sai ta yi masa sharri cewa ya so ya yi mata fyaɗe. Don haka, aka jefa shi cikin kurkuku kuma aka ɗaura shi da sarka.Farawa 39:1-20; Zabura 105:17, 18.

Yusufu bawa ne a zamanin dā, Blessing kuma baiwa ce a zamaninmu. Amma dukansu sun faɗa cikin hannun mutanen da suke sana’ar da aka daɗe ana yi, wato sayar da mutane zuwa ƙasar waje don samun kuɗi.

BABBAR SANA’A

Yaƙi shi ne hanya mafi sauƙi da mutane suke amfani da shi wajen samun bayi. An ce Sarkin Masar mai suna Thutmose na Uku ya kwashi bayi guda 90,000, bayan ya yi yaƙi da mutanen Kan’ana. Masarawan sun sa bayin aikin haƙar ma’adanai da gina haikali da kuma gina hanyar jirgin ruwa.

A lokacin Mulkin Romawa, ana samu bayi sosai sa’ad da aka yi yaƙi, kuma a wasu lokuta rashin bayi yana sa su je yaƙi. Bincike ya nuna cewa a ƙarni na farko, kusan rabin mutanen da ke ƙasar Roma bayi ne. Masarawa da kuma Romawa sun ci zalin yawancin bayinsu sosai. Alal misali, saboda wahala da kuma cin zali, tsawon rayuwar bayin da suke aiki a wurin haƙar ma’adanai na Romawa ba ya wuce shekara 30.

Da shigewar lokaci, sana’ar bayi ta ci gaba da ƙaruwa. Daga ƙarni na 16 zuwa 19, sana’ar sayar da bayi tsakanin Afirka da kuma Amirka ta zama babban sana’a sosai a duniya. Ƙungiyar Kyautata Ilimi da Kimiyya da Al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO) ta ce: ‘Bincike ya nuna cewa an kwashi maza da mata da kuma yara wajen miliyan 25 zuwa 30 kuma aka sayar da su.’ An ce dubban mutane da aka ɗauke su bayi sun mutu sakamakon hatsarin jirgin ruwa da aka yi a Tekun Atilantika. Olaudah Equiano yana ɗaya daga cikin mutanen da suka tsira kuma ya ce: “Abin da ya faru yana da ban tsoro da ba za a iya kwatanta shi ba.”

Abin tausayin shi ne, ba kawai a zamanin dā ne aka yi sana’ar bayi ba. Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya ta gano cewa har yanzu da akwai maza da mata da yara fiye da miliyan 21 da suke aiki kamar bayi kuma ana biyansu ƙanƙanin albashi. Wasu kuma ba a ma biyan su. A zamaninmu, bayi suna yin aiki a wurin haƙar ma’adinai da inda ake yin tufafi da kamfanin bulo da gidan karuwai da kuma gidajen mutane. Har yanzu ana yin wannan sana’ar ko da yake doka ta hana hakan.

Har yanzu, miliyoyin mutane suna aiki kamar bayi

SAMUN ʼYANCI

Cin zalin da aka yi wa bayi da yawa ya sa su yi yaƙi don su kwato ‘yancinsu. A ƙarni na farko kafin haihuwar Yesu, wani ɗan dambe mai suna Spartacus tare da wasu bayi guda 100,000 sun yi wa gwamnatin Roma tawaye amma ba su yi nasara ba. A ƙarni na 18, bayin da suke aiki a yankunan da ke baƙin teku na Karibiya da ke Hispaniola sun yi tawaye. Wahala da kuma cin zali da bayin suka sha yayin da suke aiki a gonar rake ya sa su yi yaƙin basasa na shekara 13. Amma a ƙarshe, mutanen Haiti sun kwato ‘yancinsu a shekara ta 1804.

A duk tarihi, ‘yancin da Isra’ilawa suka samu daga zaman bauta a Masar ne ya fi shahara. Wataƙila mutane miliyan uku ne suka samu ‘yanci daga zaman bayi a Masar. Hakika, sun cancanci samun ‘yanci. Littafi Mai Tsarki ya ce Masarawan sun sa Isra’ilawa “su yi bauta mai wuya,” kuma hakan ya kwatanta azabar da suka sha a Masar. (Fitowa 1:11-14) Wani sarkin Masar ya kafa wata doka da ta bukaci a kashe duka ‘ya’ya maza da Isra’ilawan suka haifa.Fitowa 1:8-22.

Babu wani ‘yancin da mutane suka samu a duniya da zai kai irin na Isra’ilawa. Domin Allah da kansa ne ya sa suka samu ‘yanci daga Masar. Allah ya gaya wa Musa cewa, “Na san wahalarsu, don haka na sauko in cece su.” (Fitowa 3:7, 8, Littafi Mai Tsarki) Har a yau, Yahudawa suna yin Idin Ƙetarewa don su tuna da abin da ya faru.Fitowa 12:14.

YADDA ZA A KAWO ƘARSHEN BAUTA

Littafi Mai Tsarki ya ce: “Babu mugunta a wurin Ubangiji Allahnmu,” kuma ya tabbatar mana da cewa har yanzu haka yake. (2 Labarbaru 19:7; Malakai 3:6) Allah ya aiki Yesu don ya ‘yi wa ɗaurarru shela ta saki . . . , ya kuma kwance waɗanda an ƙulle su.’ (Luka 4:18) Shin wannan ayar tana magana ne game da kowace irin bauta? A’a. Yesu ya zo ne don ya ‘yantar da mutane daga zunubi da kuma mutuwa. Daga baya ya ce: “Gaskiyar kuwa za ta ‘yantar da ku.” (Yohanna 8:32) Ko a yau, da akwai hanyoyi da yawa da gaskiyar da Yesu ya koyar take ‘yantar da mutane.—Ka duba akwatin nan “ ʼYanci Daga Wata Irin Bauta.”

Hakika, yadda Allah ya taimaka wa Yusufu ya samu ‘yanci daga bauta ya yi dabam da na Blessing. Za ka iya karanta labarin Yusufu a cikin littafin Farawa surori 39 zuwa 41. Yadda Blessing ta sami ‘yanci daga bauta yana da ban mamaki sosai.

Blessing ta je ƙasar Sifan bayan da aka kore ta daga wata ƙasar Turai. A wurin ne ta haɗu da Shaidun Jehobah kuma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da su. Domin tana so ta canja salon rayuwarta, sai ta nemi wani aiki mai kyau kuma ta roƙi uwar gidanta da ta rage yawan kuɗin da za ta riƙa biyan ta kowane wata. Wata rana, sai matar ta kira Blessing. Ta gaya mata cewa ta yafe bashin da take bin ta kuma ta ce Blessing ta gafarta mata don abin da ta yi mata. Me ya sa ta yi hakan? Domin ita ma ta soma nazarin Littafi Mai Tsarki da Shaidun Jehobah! Blessing ta ce: “Hakika, sanin gaskiya yana ‘yantar da kai a hanyoyi masu ban al’ajabi.”

Jehobah ya yi baƙin ciki don zaluncin da Isra’ilawa suka sha a Masar. Hakazalika, ba ya farin ciki da rashin adalcin da ake yi a yau. Hakika, mutane suna bukatar su canja idan ana so a daina mai da mutane bayi. Kuma Allah ya yi alkawarin cewa zai yi hakan. “Muna sauraron sababbin sammai da sabuwar duniya, inda adalci yake zaune.”2 Bitrus 3:13

^ sakin layi na 2 An canja sunan.

^ sakin layi na 3 A lokacin, farashin Euro da na dalla kusan ɗaya ne.