Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

Idan Matsaloli Sun Sa Ka Gaji da Rayuwa

Idan Matsaloli Sun Sa Ka Gaji da Rayuwa

RAYUWA akwai daɗi idan kome yana tafiya daidai. Amma, a wasu lokuta matsaloli sukan sa rayuwa ta yi wuya.

Alal misali, wata mai suna Sally * a ƙasar Amirka, wadda ta rasa mafi yawa daga cikin kayayyakinta sanadiyyar wata guguwa da aka yi, ta ce: “Na ga kamar matsalar ta fi ƙarfina kuma ba zan iya jimrewa ba.”

Wani abin da yake sa mu baƙin ciki kuma shi ne sa’ad da aka yi mana rasuwa. Wata mai suna Janice a Ostareliya, ta bayyana cewa: “Sa’ad da ’ya’yana biyu suka mutu, na yi baƙin ciki sosai. Na yi addu’a ga Allah cewa: ‘Ya Allah, na gaji da rayuwa ba zan iya jimrewa kuma ba! Gwamma in mutu.’”

Wani kuma mai suna Daniel, ya yi baƙin ciki sosai sa’ad da matarsa ta ci amanarsa. Ya bayyana cewa: “Sa’ad da matata ta ci amanata, na ji zafi sosai kamar dai an soka min wuka a zuciyata. Abin da ta yi ya sa na daɗe ina baƙin ciki.”

Wannan Hasumiyar Tsaro za ta bayyana amfanin rayuwa ko a lokacin da

Da farko, ta yaya za mu jimre sa’ad da bala’i ya abko mana?

^ sakin layi na 3 An canja wasu sunayen a talifofin nan.