Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA 40

Yadda Za A Faranta Wa Allah Rai

Yadda Za A Faranta Wa Allah Rai

ME ZA mu yi domin mu faranta wa Allah rai? Akwai abin da za mu iya ba shi ne?— Jehovah ya ce: “Kowane naman jeji nawa ne.” Kuma ya ce: “Azurfa tawa ce, zinariya kuma tawa ce.” (Zabura 24:1; 50:10; Haggai 2:8) Duk da haka, da akwai abin da za mu iya ba wa Allah. Menene wannan abin?—

Jehovah ya ƙyale mu mu zaɓi ko za mu bauta masa ko ba za mu bauta masa ba. Ba ya tilasta mana mu yi abin da yake so mu yi. Bari mu yi ƙoƙari mu fahimci abin da ya sa Allah ya yi mu yadda za mu zaɓi ko za mu bauta masa ko ba za mu bauta masa ba.

Wataƙila ka san ’yar tsana. Inji ne da aka ƙera saboda ya yi dukan abin da mai shi yake son ’yar tsanan ya yi masa. ’Yar tsanan ba shi da damar ya zaɓi abin da yake so. Jehovah yana iya halittarmu kamar ’yar tsana. Da sai ya yi mu domin mu yi abin da yake so kawai. Amma bai yi haka ba. Ka san abin da ya sa?— Wasu kayayyakin wasa ’yar tsana ne. Idan aka kunna su sai su yi abin da wanda ya ƙera su, ya ƙera su su yi. Ka taɓa ganin irin wannan abin wasa?— Sau da yawa mutane suna gajiya da abin wasa da aka ƙera shi domin ya yi abin da aka ƙera shi ya yi. Allah ba ya so mu yi masa biyayya domin mu ’yar tsana ne da aka yi mu mu bauta masa. Jehovah yana so mu bauta masa domin muna ƙaunarsa ko kuma domin muna so mu yi masa biyayya.

Me ya sa Allah bai halicce mu kamar ’yar tsana ba?

Yaya kake tsammanin Ubanmu na samaniya yake ji sa’ad da muka yi masa biyayya domin muna so mu yi masa biyayya?— Ka gaya mini, yaya halinka yake shafan iyayenka?— Littafi Mai Tsarki ya ce ɗa mai hikima yana ‘faranta wa babansa rai’ amma ɗa ‘mai wauta abin baƙin ciki ne ga mamarsa.’ (Misalai 10:1) Ka lura cewa idan ka yi abin da babanka da mamarka suke so yana faranta masu rai?— Amma yaya suke ji idan ka yi musu rashin biyayya?—

Ta yaya za ka faranta wa Jehovah da kuma iyayenka rai?

Yanzu bari mu yi tunanin Ubanmu na samaniya Jehovah. Ya gaya mana yadda za mu sa shi farin ciki. Ka ɗauko Littafi Mai Tsarki naka mu buɗe Misalai 27:11. A nan Allah yana yi mana magana: “Ɗana [za mu iya cewa ’yata], ka yi hikima, ka fa faranta zuciyata: domin in mayarda magana ga wanda ya [zolaye] ni.” Ka san abin da yake nufi a zolayi mutum?— Mutum zai iya zolayarka ta wajen yi maka dariya yana cewa ba za ka iya yin abin da ka ce za ka yi ba. Ta yaya Shaiɗan ya zolayi Jehovah?— Bari mu gani.

Ka tuna mun koya daga Babi na 8 na wannan littafin cewa Shaiɗan yana so ya zama Na Fari kuma yana so kowa ya yi masa biyayya. Shaiɗan ya ce mutane suna bauta wa Jehovah ne domin Jehovah zai ba su rai na har abada idan suka bauta masa. Bayan Shaiɗan ya sa Adamu da Hauwa’u suka yi wa Jehovah rashin biyayya, Shaiɗan ya ƙalubalanci Allah. Ya gaya wa Allah: ‘Mutane suna bauta maka ne kawai domin abin da suke samu. Ka ƙyale ni ka gani, zan sa kowa ya ƙi ka.’

Bayan Adamu da Hauwa’u suka yi zunubi, ta yaya Shaiɗan ya ƙalubalanci Jehovah?

Hakika, waɗannan kalmomin ba haka suke ba a cikin Littafi Mai Tsarki. Amma sa’ad da ka karanta labarin Ayuba, za ka ga cewa Shaiɗan ya gaya wa Allah wani abu kamar haka. Hakika yana da muhimmanci ga Shaiɗan da kuma Allah, ko Ayuba zai kasance da aminci ga Allah ko ba zai kasance ba. Bari mu buɗe Littafi Mai Tsarki mu karanta Ayuba sura 1 da ta 2 mu ga abin da ya faru.

Ka lura cewa a Ayuba sura ta 1 Shaiɗan yana sama sa’ad da mala’iku suka zo su ga Jehovah. Saboda haka, Jehovah ya tambayi Shaiɗan: “Daga ina ka fito?” Shaiɗan ya amsa ya ce ya fito ne daga yawace-yawace cikin duniya. Sai Jehovah ya tambaye shi: ‘Ka ga Ayuba, da yake bauta mini, kuma ba ya yin abin da ba shi da kyau?’—Ayuba 1:6-8.

A take Shaiɗan ya ba da hujjoji. ‘Ayuba yana bauta maka ne kawai domin ba shi da damuwa. Idan ka daina kāre shi ka daina sa masa albarka zai zage ka.’ Sai Jehovah ya amsa: ‘To, ya yi kyau, Shaiɗan, kana iya yi masa dukan abin da kake so, amma kada ka yi masa rauni.’—Ayuba 1:9-12.

Menene Shaiɗan ya yi?— Ya sa mutane suka sace shanu da jakunan Ayuba suka kuma kashe masu kula da su. Sai kuma aradu ya faɗi ya halaka tumakinsa da masu kula da su. Daga baya, mutane suka zo suka sace raƙumansa suka kashe waɗanda suke kula da su. A ƙarshe, Shaiɗan ya sa hadari ya rushe gidan da ’ya’yan Ayuba goma suka taru, kuma dukansu suka mutu. Duk da wannan, Ayuba ya ci gaba da bauta wa Jehovah.—Ayuba 1:13-22.

Sa’ad da Jehovah ya sake ganin Shaiɗan, Jehovah ya nuna yadda Ayuba yake da aminci. Shaiɗan ya ba da hujjoji: ‘Idan ka ƙyale ni na yi masa rauni, zai zage ka.’ Saboda haka Jehovah ya ƙyale Shaiɗan ya yi wa Ayuba rauni amma ya yi masa gargaɗi kada ya kashe Ayuba.

Menene Ayuba ya jimre, kuma me ya sa wannan ya faranta wa Allah rai?

Shaiɗan ya harɓi Ayuba da gyambuna a dukan jikinsa. Gyambunan suna wari ƙwarai da babu wanda yake so ya zo kusa da shi. Har matar Ayuba ta ce masa: ‘Ka zagi Allah ka mutu!’ Waɗanda suka ce su abokanan Ayuba ne suka ziyarce shi suka sake daɗa masa baƙin ciki suka ce ya yi mugun abu ne ya sa yake shan irin wannan wahala. Duk da wahala da azaba da Shaiɗan ya ba Ayuba, Ayuba ya ci gaba da bauta wa Jehovah cikin aminci.—Ayuba 2:1-13; 7:5; 19:13-20.

Yaya kake jin amincin Ayuba ya sa Jehovah ya ji?— Ya sa ya yi farin ciki domin Jehovah ya gaya wa Shaiɗan: ‘Dubi Ayuba! Yana bauta mini ne domin yana so ya bauta mini.’ Za ka zama kamar Ayuba, mutumin da Jehovah zai nuna ya ba da misali da ya tabbatar da Shaiɗan maƙaryaci ne?— Hakika, gata ce a ba da amsa ga Shaiɗan da ya yi da’awar cewa zai iya ya sa kowa ya ƙi bauta wa Jehovah. Hakika Yesu ya ga wannan gata ce.

Babban Malami bai taɓa ƙyale Shaiɗan ya sa shi ya yi abin da ba daidai ba. Ka yi tunanin yadda misalinsa ya sa Ubansa farin ciki! Jehovah zai iya ba da amsa ga Shaiɗan: ‘Dubi Ɗana! Ya kasance da cikakken aminci domin yana ƙaunata!’ Ka yi tunanin yadda Yesu kuma yake murna wajen faranta wa Ubansa rai. Domin wannan farin cikin, Yesu ya jimre mutuwa a kan gungume na azaba.—Ibraniyawa 12:2.

Kana so ka zama kamar Babban Malaminmu kuma ka faranta wa Jehovah rai?— To sai ka ci gaba da koyo game da abin da Jehovah yake so ka yi, kuma ka faranta masa rai ta wajen yin haka!

Ka karanta abin da Yesu ya yi ya faranta wa Allah rai da kuma abin da muke bukatar mu yi mu ma, a Misalai 23:22-25; Yohanna 5:30; 6:38; 8:28; da kuma 2 Yohanna 4.