Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

BABI NA GOMA SHA TAKWAS

Ta Yi ‘Bimbini a Cikin Zuciyarta’

Ta Yi ‘Bimbini a Cikin Zuciyarta’

1, 2. Ka bayyana tafiyar da Maryamu ta yi da kuma abin da ya sa hakan ba ta da sauƙi?

MARYAMU ta gyara zama a kan jaki da kyar domin tana da nauyi. Ta kwashe sa’o’i da yawa tana tafiya. Yusufu kuma yana gaba yana jan jakin. Maryamu ta ji jariri yana motsi a cikinta.

2 Kamar yadda Littafi Mai Tsarki ya nuna, Maryamu ta kusan haihuwa. (Luk 2:5, 6) Yayin da suke wuce gona ɗaya bayan ɗaya, wataƙila manoma sun kalle ta suna mamakin abin da ya sa mace da ta kusan haihuwa take irin wannan doguwar tafiya. Me ya sa Maryamu take wannan doguwar tafiya daga birnin Nazarat?

3. Wane aiki ne aka ba Maryamu, kuma me za mu koya game da ita?

3 Abin da ya faru watanni da yawa da suka shige ne ya jawo hakan. An ba Maryamu wani aiki mai muhimmanci sosai. Za ta haifi ɗa da zai zama Almasihu, wato Ɗan Allah! (Luk 1:35) Sa’ad da ta kusan haihuwa ne bukatar yin wannan tafiyar ta taso. A sakamako, ta fuskanci ƙalubale da yawa ga imaninta. Bari mu tattauna abin da ya taimake ta ta kasance da bangaskiya sosai.

Tafiya Zuwa Bai’talami

4, 5. (a) Me ya sa Yusufu da Maryamu suke tafiya zuwa Bai’talami? (b) Wane annabci ne shelar da Kaisar ya yi ya cika?

4 Ba Yusufu da Maryamu kaɗai ba ne suke wannan tafiyar ba. Kaisar Augustus ya ba da umurni cewa kowane mazaunin ƙasar ya koma garinsa don a yi ƙidayarsa. Mene ne Yusufu ya yi? Littafi Mai Tsarki ya ce: “Yusufu kuma ya tashi daga Galili, daga cikin birnin Nazarat, zuwa Yahudiya, zuwa birnin Dawuda, wanda ake ce da shi Bai’talami; domin shi daga gida da dangin Dawuda ne.”—Luk 2:1-4.

5 Wani annabcin da aka yi kusan shekara 700 kafin wannan lokacin ya ce za a haifi Almasihu a Bai’talami. Saboda haka, shelar da Kaisar ya yi a wannan lokacin ba kuskure ba ce. Akwai wani gari mai nisan mil bakwai daga Nazarat da ake kira Bai’talami. Amma, annabcin ya faɗa takamaimai cewa za a haifi Almasihu a “Bai’talami Ephrathah.” (Karanta Mikah 5:2.) Idan kana so ka kai wannan ƙaramin ƙauyen daga Nazarat, za ka bi ta Samariya kuma za ka yi tafiyar mil 80 a hanya mai tuddai. Ƙauyen Bai’talami da Yusufu ya je ke nan, kuma nan ne zuriyar Sarki Dauda suke. Yusufu da Maryamu ’yan ƙauyen ne.

6, 7. (a) Me ya sa tafiya zuwa Bai’talami ta yi wa Maryamu wuya? (b) Ta yaya zama matar Yusufu ya shafi rayuwar Maryamu? (Ka kuma duba hasiya.)

6 Shin Maryamu za ta goyi bayan Yusufu kuwa? Ballantana ma, za ta ji jiki a tafiyar. Wataƙila an soma shiga lokacin damina kuma an ɗan yi yayyafi. Ƙari ga haka, yin tafiya zuwa Bai’talami zai kasance mata da wuya sosai domin garin yana kan tudu. Wataƙila, za su riƙa hutawa a hanya kuma hakan zai ci lokaci sosai. Kowace mace da ta kusan haihuwa za ta so ta kasance kusa da iyalinta da ƙawayenta don su taimaka mata sa’ad da take naƙuda. Babu shakka, Maryamu tana bukatar gaba gaɗi don ta yi wannan tafiyar.

Tafiya zuwa Bai’talami ba cin tuwo ba ne

7 Bugu da ƙari, littafin Luka ya ce Yusufu ya je ya yi ƙidayar “kansa tare da Maryamu.” Ya kuma ce Yusufu ya auri Maryamu wadda “yana tashinta.” (Luk 2:4, 5) Zama matar Yusufu ya shafi rayuwar Maryamu sosai. Maryamu tana ɗaukan mijinta a matsayin mai ja-gorar bautarsu ga Jehobah kuma ta amince da hakkin da Allah ya danƙa mata a matsayin mataimakiyarsa don tana tallafa masa wajen tsai da shawarwari. * Maryamu ta nuna bangaskiya a yadda ta yi biyayya ga mijinta.

8. (a) Mene ne wataƙila ya kuma sa Maryamu ta je Bai’talami tare da Yusufu? (b) A wace hanya ce misalin Maryamu ya zama abin ƙarfafa a gare mu?

8 Mene ne wataƙila kuma ya sa Maryamu ta yi biyayya? Shin ta san annabcin da aka yi cewa za a haifi Almasihu a Bai’talami? Littafi Mai Tsarki bai ce ba, amma mai yiwuwa, Maryamu ta san da annabcin, tun da yawancin mutane a lokacin sun sani. (Mat. 2:1-7; Yoh. 7:40-42) Ƙari ga haka, Maryamu ta san Nassosi sosai. (Luk 1:46-55) Ko da Maryamu ta yi tafiyar don ta yi biyayya ga mijinta ko don shelar da Kaisar ya yi ko don annabcin Jehobah ko kuma don dukan dalilan nan, ta kafa mana misali mai kyau. Jehobah yana daraja maza da mata masu tawali’u da kuma biyayya. Misalin Maryamu yana ƙarfafa mu sosai, duk da cewa yawancin mutane a yau suna rashin biyayya.

An Haifi Kristi

9, 10. (a) Wane tunani ne wataƙila Maryamu da Yusufu suka yi yayin da suka yi kusa da Bai’talami? (b) Me ya sa Yusufu da Maryamu suka sauka a barga?

9 Maryamu ta yi farin ciki sa’ad da ta hangi Bai’talami daga nesa. Sa’ad da suke hawan tuddai, wataƙila Maryamu da Yusufu sun tuna da tarihin ƙauyen yayin da suke wuce gonakin anab, wanda ɗaya ne cikin shuke-shuken da ake girbewa a ƙarshe. Ba a ambata wannan ƙauyen cikin biranen Yahuda ba domin ya yi ƙanƙanta ainun kamar yadda annabi Mikah ya annabta. Amma fiye da shekara dubu kafin wannan zamanin, an haifi Baoz da Naomi da kuma Dauda a wannan ƙauyen.

10 Maryamu da Yusufu sun sami ƙauyen cike da mutane. Wasu sun riga su zuwa ƙidayar, shi ya sa ba su sami masauki ba. * Hakan ya sa suka sauka a barga. Ka yi tunanin yadda Yusufu ya damu sa’ad da matarsa ta soma naƙuda a bargar.

11. (a) Me ya sa kowace mace za ta ji tausayin Maryamu? (b) A waɗanne hanyoyi ne Yesu ya zama “ɗan fari”?

11 Mata a ko’ina za su fahimci yanayin da Maryamu take ciki. Shekaru 4,000 da suka shige, Jehobah ya ce mata za su riƙa shan wahala sa’ad da suke haihuwa sanadin zunubi. (Far. 3:16) Hakan kuma ya haɗa da Maryamu. Amma, littafin Luka bai kwatanta wahalar da ta sha ba, maimako, ya ce: “Ta kuwa haifi ɗan farinta.” (Luk 2:7) Hakika, ta sami ɗanta na fari kuma daga baya ta sake haifar aƙalla ’ya’ya shida. (Mar. 6:3) Babbu shakka, wannan zai yi fice da sauran. Ban da cewa shi ɗanta na fari ne, shi kuma “ɗan fari ne gaban dukan halitta,” wato ɗa makaɗaici na Allah!—Kol. 1:15.

12. A wane wuri ne Maryamu ta kwantar da ɗanta, kuma yaya hakan ya yi dabam da zane-zane da kuma fina-finan da ake yi a yau?

12 A wannan lokacin ne ayar ta yi wani bayani mai muhimmanci: “Ta rufe shi da zanen goyo, ta kuma kwantar da shi a wani komin dabbobi.” (Luk 2:7, Littafi Mai Tsarki) Mutane da yawa a faɗin duniya suna ƙara gishiri a hotuna dabam-dabam da suke zanawa da kuma fina-finan da suke yi game da wannan batun. Amma mene ne ainihin gaskiyar batun? Ka tuna cewa barga da suka sauka ba wuri mai tsabta ba ce. Hakika, babu iyayen da za su so su haifi ɗansu ko ’yarsu a irin wannan wurin idan akwai wasu wurare masu kyau. Yawancin iyaye suna son su haifi ɗansu ko ’yarsu a wuri mafi kyau. Hakazalika, Maryamu da Yusufu ma suna son a haifi Ɗan Allah a wuri mafi kyau!

13. (a) Ta yaya Maryamu da Yusufu suka yi iya ƙoƙarinsu a yanayin da suka sami kansu? (b) Ta yaya iyaye masu hikima a yau za su iya yin koyi da Yusufu da kuma Maryamu?

13 Ba su ƙyale wannan yanayin ya dame su ba, amma sun yi iya ƙoƙarinsu a yanayin da suka sami kansu. Alal misali, ka tuna cewa Maryamu ta kula da jaririn da kanta, ta rufe shi da zanen goyo kuma ta kwantar da shi a komin dabbobi. Maryamu ta tabbata cewa sanyi bai shiga jikinsa ba kuma ta kāre shi. Duk da yanayin da suke ciki, ta yi iya ƙoƙarinta don ta kula da yaron. Ita da Yusufu sun kuma san cewa koya masa game da Jehobah ne abu mafi muhimmanci. (Karanta Kubawar Shari’a 6:6-8.) Abin da iyaye da yawa a yau suka fi mai da wa hankali ke nan a wannan duniyar da babu ruwan yawancin mutane da Allah.

Makiyayan Sun Ƙarfafa Su

14, 15. (a) Me ya sa makiyayan suka yi ɗokin ganin jaririn? (b) Mene ne makiyayan suka yi bayan sun ga jaririn a barga?

14 Wani abu ya faru farat ɗaya da ya ta da hankalin mutane. Wasu makiyaya sun shigo bargar da sauri don su ga iyalin da kuma yaron musamman. Waɗannan mazajen suna matuƙar farin ciki. Sun taho ne daga tudu inda suke kiwon dabbobinsu. * Sun gaya wa iyayen abin mamaki da suka shaida. Wani mala’ika ya bayyana ga makikayan farat ɗaya da tsakar dare a kan tudun da suke zama. Darajar Jehobah ta haskaka ko’ina kuma mala’ikan ya gaya musu cewa an haifi Kristi, wato Almasihu a Bai’talami. Ya ce za su ga yaron kwance cikin komin dabbobi lulluɓe da zane. Sai wani abu mafi ban mamaki ya faru, mala’iku masu dimɓin yawa suka bayyana, suna yabon Allah!—Luk 2:8-14.

15 Shi ya sa waɗannan maza masu tawali’u suka shigo Bai’talami da gaggawa. Babu shakka, sun yi farin cikin ganin jariri kwance kamar yadda mala’ikan ya faɗa. Ba su yi gum da bakinsu ba. Littafi Mai Tsarki ya ce: Sun “bada labarin batun . . . Dukan waɗanda suka ji suka yi al’ajabi da al’amuran da aka faɗa musu ta bakin makiyaya.” (Luk 2:17, 18) A wannan zamanin, limamai ba sa daraja makiyaya, amma Jehobah yana daraja su domin suna da tawali’u da kuma aminci. Ta yaya wannan ziyarar ta shafi Maryamu?

16. Ta yaya Maryamu ta nuna cewa tana lura sosai, kuma yaya hakan ya shafi rayuwarta?

16 Babu shakka, naƙudar da Maryamu ta yi ya gajiyar da ita tikis, amma duk haka, ta saurara sosai. Ƙari ga hakan, “Maryamu ta ādana waɗannan al’amura, tana bimbinin su a cikin zuciyarta.” (Luk 2:19) Hakika, wannan macen tana lura sosai. Ta san cewa saƙon wannan mala’ikan yana da muhimmanci. Jehobah yana so ta san asali da kuma muhimmancin ɗanta. Maryamu ba ta saurara kaɗai ba, amma ta adana su a cikin zuciyarta don ta riƙa yin bimbini a kansu. Shi ya sa ta kasance da bangaskiya muddar ranta.—Karanta Ibraniyawa 11:1.

Maryamu ta saurari makiyayan sosai kuma ta adana maganarsu a zuciyarta

17. Ta yaya za mu iya yin koyi da misalin Maryamu a ibadarmu?

17 Shin za ka yi koyi da Maryamu kuwa? Jehobah ya sa an rubuta gaskiya masu tamani cikin Kalmarsa, Littafi Mai Tsarki. Amma waɗannan gaskiyar ba za su amfane mu ba sai idan muka bi su. Ta yaya za mu iya yin hakan? Ta wajen karanta Littafi Mai Tsarki a kai a kai, domin ba littafin tatsuniya ba ne amma hurarriyar Kalmar Allah ce. (2 Tim. 3:16) Muna bukatar mu koya da kuma tuna da gaskiya game da Jehobah kuma mu riƙa yin bimbini a kanta. Idan muka yi bimbini a kan abin da muka koya daga Littafi Mai Tsarki kuma muka bi su, za mu ƙarfafa bangaskiyarmu sosai.

Ba Ta Manta da Maganar Ba

18. (a) A wace hanya ce Maryamu da Yusufu suka bi Dokar Allah sa’ad da Yesu yake jariri? (b) Shin hadayar da suka miƙa ta nuna cewa su mawadata ne? Ka bayyana.

18 Sa’ad da jaririn ya kai kwana takwas, Maryamu da Yusufu sun yi masa kaciya kamar yadda Doka ta ce, kuma sun sa masa suna Yesu kamar yadda aka umurce su. (Luk 1:31) Sa’an nan a kwana na arba’in, suka kai shi haikalin da ke Urushalima wanda ke da nisan mil shida daga Bai’talami. Yusufu da Maryamu sun miƙa hadaya ta tsarkakewa kamar yadda Dokar ta ce. Sun ba da kurciya biyu ko ’yan tantabaru biyu domin su talakawa ne. Ko da Yusufu da Maryamu sun ji kunya amma duk da haka, sun yi biyayya ga Dokar Allah gwargwadon ƙarfinsu. Sun samu ƙarfafa sosai sa’ad da suka je wurin.—Luk 2:21-24.

19. (a) Mene ne Siman ya ce da Maryamu ta adana a zuciyarta? (b) Mene ne Hannatu ta yi sa’ad da ta ga Yesu?

19 Wani dattijo mai suna Siman ya zo wurinsu kuma ya faɗi wasu kalmomin da Maryamu ta adana a cikin zuciyarta. An yi wa Siman alkawari cewa ba zai mutu ba sai bayan ya ga Almasihu kuma ruhu mai tsarki na Jehobah ya sanar masa cewa Yesu ne Mai-ceto da aka yi alkawarinsa. Siman ya kuma gaya wa Maryamu baƙin cikin da za ta yi wata rana. Ya ce za ta ji kamar an tsaga zuciyarta da takobi. (Luk 2:25-35) Ko da wannan gargaɗi ne game da abu marar kyau da Maryamu za ta shaida, amma ya taimaka mata ta jimre sa’ad da hakan ya faru bayan shekara 33. Ban da Siman, akwai wata annabiya mai suna Hannatu da ta ga Yesu sa’ad da yake jariri kuma ta yi shelarsa ga kowane mutum da ke son a fanshi Urushalima.—Karanta Luka 2:36-38.

Maryamu da Yusufu sun sami ƙarfafa a haikalin Jehobah da ke Urushalima

20. Ta yaya Yusufu da Maryamu suka amfana don sun kai ɗansu haikali a Urushalima?

20 Yusufu da Maryamu sun kawo jaririn Urushalima kuma hakan ya dace! Wannan ne lokaci na farko da Yesu ya je haikalin Allah kuma ya ci gaba da yin hakan muddar ransa. Sa’ad da suke haikalin, sun miƙa hadaya gwargwadon ƙarfinsu kuma sun sami shawara da kuma ƙarfafa. Babu shakka, abubuwan da Maryamu ta shaida a ranar sun daɗa ƙarfafa bangaskiyarta, ta sami gaskiya masu tamani da za ta yi bimbini a kai kuma za ta tattauna da mutane.

21. Ta yaya za mu tabbata cewa mun kasance da bangaskiya sosai kamar Maryamu?

21 Yadda iyaye a yau suke bin wannan misalin yana da kyau. Iyaye waɗanda Shaidun Jehobah ne suna kai yaransu taron Kirista. Waɗannan iyayen suna furta kalmomi masu ƙarfafawa ga ’yan’uwansu kuma suna hakan gwargwadon ƙarfinsu. Bayan taro, suna farin ciki da gaba gaɗi kuma suna koyan yadda za su ƙarfafa wasu. Kasancewa da su abu ne mai kyau sosai! Idan muka yi hakan, za mu kasance da bangaskiya sosai kamar Maryamu.

^ sakin layi na 7 Ka yi la’akari da bambancin da ke tsakanin wannan labarin da kuma wanda aka ambata ɗazu cewa “Maryamu kuwa ta tashi . . . ta tafi” wurin Alisabatu. (Luk 1:39) A wannan lokacin ba ta auri Yusufu ba tukun, ƙila ba ta nemi izinin sa ba kafin ta je wurin ta. Amma yanzu da sun yi aure, Yusufu ne ke da ikon tsai da shawarar tafiya ba Maryamu ba.

^ sakin layi na 10 Gama gari ne a wannan zamanin a yi tanadin masauki don matafiya.

^ sakin layi na 14 Da yake waɗannan makiyayan suna kiwon dabbobinsu a waje, hakan ya tabbatar da abin da lissafin Littafi Mai Tsarki ya nuna. Da yake makiyayan suna a waje ba a cikin gida ba, ya nuna cewa an haifi Yesu a farkon watan Oktoba ba watan Disamba ba.

Jehobah ya daraja waɗannan makiyaya masu tawali’u da kuma aminci