Koma ka ga abin da ke ciki

Koma ga abubuwan da ke ciki

DARASI NA 13

Yakubu da Isuwa Sun Shirya

Yakubu da Isuwa Sun Shirya

Jehobah ya yi wa Yakubu alkawari cewa zai kāre shi yadda ya kāre Ibrahim da Ishaƙu. Yakubu ya kama zama a ƙasar Haran. A nan ne ya yi aure, ya sami yara da yawa kuma ya yi arziki sosai.

Daga baya, sai Jehobah ya ce wa Yakubu: ‘Ka koma ƙasarku.’ Sai Yakubu da iyalinsa suka soma tafiya mai nisa. Sa’ad da suke hanya, sai bayin Yakubu suka zo suka gaya masa cewa: ‘Ɗan’uwanka Isuwa yana zuwa tare da mutanensa ɗari huɗu.’ Tsoro ya kama Yakubu domin yana tunanin cewa Isuwa yana so ya kashe shi da iyalinsa. Sai ya yi addu’a ga Jehobah, ya ce: ‘Ina roƙonka, ka cece ni daga hannun ɗan’uwana.’ Washegari, sai Yakubu ya aika wa Isuwa kyautar tumaki da awaki da shanu da rakuma da kuma jakai.

Da dare sa’ad da Yakubu yake shi kaɗai, sai ya ga wani mala’ika. Shi da mala’ikan suka soma kōkawa har safe. Ko da yake Yakubu ya ji ciwo, amma ya ƙi ya saki mala’ikan. Sai mala’ikan ya ce: ‘Ka sake ni.ʼ Amma Yakubu ya ce: ‘Ba zan sake ka ba, sai ka albarkace ni.’

Bayan haka, sai mala’ikan ya albarkaci Yakubu. A lokacin ne Yakubu ya san cewa Jehobah ba zai ƙyale Isuwa ya yi masa wani abu ba.

A ranar da safe, Yakubu ya ga Isuwa da mutanensa ɗari huɗu daga nesa. Sai Yakubu ya bar iyalinsa a baya, ya je ya rusuna a gaban Isuwa sau bakwai. Isuwa ya zo da gudu ya rungumi Yakubu. Sai su biyu suka soma kuka kuma suka shirya. Yaya kake gani Jehobah ya ji saboda yadda Yakubu ya bi da wannan yanayin?

Daga baya, sai dukansu suka koma gidajensu. Yakubu yana da yara maza guda goma sha biyu. Sunansu Reuben da Simeon da Lawi da Yahuda da Dan da Naphtali da Gad da Asher da Issachar da Zebulun da Yusufu da kuma Banyamin. Jehobah ya yi amfani da ɗaya daga cikinsu mai suna Yusufu wajen ceton mutanensa. Ka san yadda ya yi hakan? Za mu koyi hakan a babi na gaba.

“Ku ƙaunaci waɗanda ba sa ƙaunarku, ku yi wa masu tsananta muku addu’a. Ta yin haka ne za ku zama ’ya’yan Ubanku na sama.”​—Matta 5:​44, 45, Juyi Mai Fitar da Ma’ana