Koma ka ga abin da ke ciki

15 GA JANAIRU, 2020
PUERTO RICO

Girgizar Kasa Mai Karfi ta Afka wa Puerto Rico

Girgizar Kasa Mai Karfi ta Afka wa Puerto Rico

A ranar 7 ga Janairu, 2020, girgizar kasa mai maki 6.4 ta afka wa kasar Puerto Rico. Bayan haka, an yi kananan girgizar kasa fiye da dari. A safiyar ranar 11 ga Janairu, 2020, wata girgizar kasa mai maki 5.9 ta sake afka wa tsibirin.

Ana taro a wata ikilisiya a Castañer, Lares, duk da cewa babu wutar lantarki

Mutane da yawa da ke yankunan ba su da lantarki kuma suna kwana a waje don tsoro. Ofishinmu da ke Amirka ya ce babu wani dan’uwanmu da ya jikkata ko kuma ya rasa ransa. Amma ʼyan’uwa 248 sun bar gidajensu. Kari ga haka, girgizar kasar ta rushe gidaje 8 na ʼyan’uwa kuma ta bata guda 70. Ta kuma bata Majami’un Mulki guda goma. Kwamitin Aikin Agaji da masu kula da da’ira suna shirya kayan agaji kuma suna karfafa masu shela da bala’in ya shafa.

Duk da kalubalen nan, ʼyan’uwanmu sun ci gaba da bauta wa Jehobah. Dan’uwa Robert Hendriks da ke tsara ayyukan Sashen da Ke Samo Labarai a Reshen Amirka, ya ce: “Hankulan ʼyan’uwa a Puerto Rico ya tashi sosai domin ba a saba yin irin wannan bala’in ba. Amma muna farin ciki cewa hakan bai sa su sanyin gwiwa ba. Sun ci gaba da yin taro da kuma wa’azi duk da cewa ba su da wutar lantarki da kuma ruwa. Dattawa suna aiki gadan-gadan don su taimaka da kuma karfafa mabukata.”

ʼYan’uwa da yawa suna kwana a waje don za a iya sake girgizar kasa

Yadda ʼyan’uwa suke mai da hankali ga abubuwa na ibada duk bala’in nan, yana burge mu sosai. Muna addu’a cewa Jehobah ya ci gaba da sa su kasance da kwanciyar rai.​—Zabura 119:165.