Koma ka ga abin da ke ciki

12 GA YUNI, 2020
LABARAN DUNIYA

’Yan’uwanmu a Ruwanda da Zimbabuwe Sun Sami Abinci a Lokacin Annobar Koronabairas

’Yan’uwanmu a Ruwanda da Zimbabuwe Sun Sami Abinci a Lokacin Annobar Koronabairas

Ofisoshinmu da ke Ruwanda da Zimbabuwe da kuma dattawa da ke ikilisiyoyin yankin suna aiki tukuru don su tabbatar da cewa ’yan’uwanmu da ba su da isashen abinci a wannan lokacin annobar koronabairas sun sami abinci.

Ruwanda

A ranar 2 ga Afrilu 2020, Kwamitin da ke kula da ofishinmu da ke Ruwanda ya tura sako ga dattawan da ke ikilisiyoyin yankin cewa su nemi ’yan’uwa da ba su da abin biyan bukata sakamakon annobar koronabairas don a taimaka musu. Da suka sami wannan umurnin, dattawa a fadin kasar sun yi shiri don su taimaka wa ’yan’uwan da ba su da isashen abinci da sauran abin biyan bukata.

Bayan wajen sati biyu, ofishinmu na Ruwanda ya kafa Kwamitin Ba da Agaji guda 31. Kwamitocin sun ba ’yan’uwa abinci kamar su garin masara da shinkafa da wake da gishiri da sukari da kuma mai. A yanzu, an taimaka wa iyalai fiye da 7,000 ta wajen ba su kayan agaji.

Bayan da a ka ba wa ’Yar’uwa Nizeyimana Charlote abinci, ita da ’ya’yanta uku sun ce: “Muna muku matukar godiya yadda kuke tanadar mana da abinci kuma kuna karfafamu da Kalmar Allah a wannan lokacin da muke fama da annobar koronabairas. Ba za mu iya kwatanta irin farin cikin da muke yi ba.”

A ranar da aka ba wani dan’uwa da iyalinsa abinci, ya ce: “A wannan ranar, matata ta suma saboda da yunwa. Nan take, sai wani dan’uwa ya kira ni ya ce zan iya zuwa in karbi abinci. Na yi mamaki ba kadan ba. A daren, na yi ta addu’a ina gode wa Jehobah.”

Zimbabuwe

Kasarmu tana fama da yunwa kafin a soma annobar koronabairas.

Ofishinmu da ke Zimbabuwe ya kafa Kwamitin Ba da Agaji guda biyar don su taimaka wa ’yan’uwa. Ban da haka, ’yan’uwa da ke ofishinmu sun gaya wa ’yan’uwa da suke da abinci su yi gudummawar abinci don a ba wadanda ba su da shi. Sai Kwamitin Ba da Agaji suka rarraba ma wadanda ke da bukatar abincin.

Tun daga lokacin zuwa yanzu, Kwamitin Ba da Agaji ya rarraba kilo 62,669 na garin masara, da lita 6,269 na mai, da kilo 3,337 na busashen kifi, da kuma kilo 5,139 na wake ga masu shela 7,319.

Wasu ma’aurata da ke nazarin Littafi Mai Tsarki kuma suna halartan taro a kullum sun bukaci abinci. Sun yi farin ciki sosai sa’ad da wadanda suna nazari da su suka ba su abinci. Kafin a ba su abincin, faston cocinsu ya kira su yana rokan su su yi masa gudummawa saboda ya iya sayan abinci ma iyalinsa. Da ma’auratan suka ga bambanci da ke tsakanin Shaidun Jehobah da fastonsu, sai suka rubuta wa cocinsu wasika cewa sun daina zama membobin cocin.

Babu shakka, Jehobah zai ci gaba da sa albarka ga aikin agaji da ake yi, kuma muna da tabbaci cewa ’yan’uwanmu da ke Ruwanda da Zimbabuwe za su ci gaba da samun abubuwan biyan bukata.​—⁠Ayyukan Manzanni 11:⁠29.