Koma ka ga abin da ke ciki

Ɗalibai Sun Gaskata Cewa Yesu Ya Taɓa Wanzuwa Kuwa?

Ɗalibai Sun Gaskata Cewa Yesu Ya Taɓa Wanzuwa Kuwa?

 Ɗalibai suna da ƙarfafar dalilin gaskata da cewa Yesu ya wanzu. Wani rubutu da ’yan tarihi suka yi a ƙarnuka na farko da na biyu game da Yesu da kuma Kiristoci na farko, juyin 2002 na Encyclopædia Britannica, ya ce: “Wannan tarihin ya nuna cewa ko maƙiyan Kiristoci ma ba su yi musun Yesu yana cikin tarihi ba, wanda kuwa aka yi musunsa da farko ba tare da wani dalili ba a ƙarshen ƙarni na 18, a cikin ƙarni na 19, da kuma a farkon ƙarni na 20.”

 A shekara ta 2006, littafin nan Jesus and Archaeology ya ce: “Babu wani ɗalibi a yau da ke musun cewa wani Bayahudi da ake kira Yesu ɗan Yusufu ya taɓa rayuwa; yawancin mutane sun amince yanzu cewa mun ɗan san wani abu game da ayyukansa da kuma koyarwarsa ta musamman.”

 Littafi Mai Tsarki ya bayyana Yesu cewa ainihin mutum ne. Ya ba da tarihin zuriyarsa da kuma iyalinsa. (Matta 1:1; 13:55) Ya kuma ba da sunayen masu sarauta da ke tsaran Yesu ne. (Luka 3:1, 2) Waɗannan bayanin sun sa ’yan bincike su tabbatar da gaskiyar tarihin Littafi Mai Tsarki.