Koma ka ga abin da ke ciki

Wane Irin Littafi Ne Baibul?

Wane Irin Littafi Ne Baibul?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Kananan littattafai guda 66 ne aka harhada suka zama Baibul. An yi wajen shekaru 1,600 ana rubuta su. Baibul “kalmar Allah” ce, wato maganar Allah ce ga ꞌyan Adam.​—1 Tasalonikawa 2:13.

A wannan talifin, za mu tattauna:

 Muhimman bayanai game da Baibul

  •   Su wa suka rubuta Baibul? Allah ne mawallafin Baibul, amma ya yi amfani da mutane wajen 40 su rubuta shi. Wasu cikin mutanen nan su ne Musa, da Sarki Dauda, da Matiyu, da Markus, da Luka, da kuma Yohanna. a Allah ya saka sakonsa a zukatan mutanen nan, saꞌan nan suka rubuta shi.​—2 Timoti 3:16.

     Alal misali, idan wani dan kasuwa ya ce ma sakatarensa ya rubuta masa wasika kuma ya gaya masa abin da zai rubuta, dan kasuwan ne yake da wasikar. Haka ma, ko da yake Allah ya yi amfani da mutane su rubuta Baibul, littafin da sako da ke ciki, nasa ne.

  •   Mene ne kalmar nan “Baibul” take nufi? Kalmar nan “Baibul” daga yaren Girka aka samo ta. Asalin kalmar ita ce biblia, kuma tana nufin kananan littattafai. A kwana a tashi, da aka hada kananan littattafan da suke cikin Baibul suka zama littafi guda, shi ma sai aka ce da shi biblia.

  •   Wane lokaci ne aka rubuta Baibul? A shekara ta 1513 kafin haihuwar Yesu ne aka soma rubuta Baibul. Kuma a wajen shekara ta 98 bayan haihuwar Yesu ne aka kammala rubutun littafinsa na karshe. Wato fiye da shekaru 1,600 bayan lokacin da aka soma rubuta Baibul ke nan.

  •   Ina Baibul da aka fara rubutawa yake? Ba mu da littattafan Baibul da aka rubuta da farko a yau. Me ya sa? Domin abubuwa da ake rubutu a kai a lokacin sukan lalace da shigewar lokaci. Wasu takardun da wani irin ciyawa da ake kira papyrus ne aka yi su, wasu kuma da fatar dabbobi. Amma kafin su lalace, kwararun marubuta sun natsu sosai sun yi ta kofan rubutun da ke ciki suna sakawa a sabbin takardu domin mutane su samu su karanta a nan gaba.

  •   Me ake nufi da “Tsohon Alkawari” da “Sabon Alkawari”? Bangaren Littafi Mai Tsarki da yawancinsa da Ibrananci aka rubuta, shi ne mutane suke kira Tsohon Alkawari. b Ana kuma ce da shi Nassosin Ibrananci. Wanda aka rubuta da yaren Girka kuma shi ne mutane suke kira Sabon Alkawari. Ana kuma ce da shi Nassosin Helenanci na Kirista. An hada su biyun a littafi daya kuma ana ce da shi Nassosi Masu Tsarki ko Littafi Mai Tsarki. c

  •   Me da me ke cikin Baibul? Baibul yana dauke da tarihi, da dokoki, da annabce-annabce, da wakoki, da karin magana, da wasiku.​—Ka duba “ Sunayen littattafan da ke cikin Baibul.”

 Me da me Baibul ya yi magana a kai?

 A farko-farkon Baibul, bayanin yadda Allah Madaukaki ya halicci sama da kasa aka yi. Allah ya kuma yi amfani da Baibul don ya sanar da mu ko wane ne shi, ya gaya mana sunansa kuma ya bayana cewa yana so mutane su san shi.​—Zabura 83:18.

 Baibul ya bayana cewa Shaidan ya bata sunan Allah a gaban halittunsa, saꞌan nan ya nuna yadda Allah zai wanke kansa daga zargin da aka yi masa.

 Baibul ya nuna yadda Allah ya so duniya ta kasance, da kuma yadda ya so rayuwarmu ta kasance. Ya sake nuna yadda Allah zai kawar da wahala da mutane suke sha.

 Baibul yana dauke da shawara mai kyau a kan rayuwarmu. Ga wasu cikinsu:

  •   Yadda mutum zai zauna lafiya da mutane. “Duk abin da kuke so mutane su yi muku sai ku ma ku yi musu.”​—Matiyu 7:12.

     Abin da hakan yake nufi: Mu dinga kyautata wa mutane, kamar yadda za mu so su ma su kyautata mana.

  •   Yadda mutum zai rage yawan damuwa. “Kada ku damu domin gobe, gama gobe yana zuwa da wahalolinsa, wahalolin yau sun ishe ku domin yau.”​—Matiyu 6:34.

     Abin da hakan yake nufi: Maimakon mu yi ta damuwa a kan abin da bai faru ba tukun, gwamma mu bari mu fuskanci matsalar da ke a gabanmu yanzu.

  •   Yadda mutum zai ji jadin aurensa. “Bari kowane dayanku ya kaunaci matarsa kamar kansa, ita matar kuwa ta girmama mijinta.”​—Afisawa 5:33.

     Abin da hakan yake nufi: Mata da miji suna bukatar su nuna wa junansu kauna da bangirma idan suna so su ji dadin aurensu.

 An canja abin da aka rubuta a Baibul?

 Aꞌa. Masu bincike sun yi nazari sosai, sun gwada abin ke Baibul da muke da shi a yau da abin da ke rubuce-rubucen Baibul da suke nan tun dā, kuma sun ga cewa ba a canja ainihin sako da ke cikinsa ba. Haka ya kamata ya kasance. Domin idan har Allah yana so mutane su karanta wannan sakon kuma su fahimce shi, ai ba zai bari a canja shi ba. d​—Ishaya 40:8.

 Me ya sa ake da fassarar Baibul iri-iri?

 Baibul yana dauke da “labari mai dadi” domin “kowace al’umma, da zuriya, da yare.” (Ru’uyar da Aka Yi wa Yohanna 14:6) Amma yawancin mutane a yau ba sa fahimtar asalin yarukan da aka rubuta Baibul da su. Saboda haka, mutane suna bukatar fassarar Baibul a harshen da za su iya fahimta don su iya karanta shi kuma su fahimci abin da Allah yake so su sani.

 Akwai hanyoyin fassara Littafi Mai Tsarki guda uku:

  •   Wasu sukan fassara kowace kalma daidai yadda take ko da maꞌanar ba daya ba ne a yarensu.

  •   Wasu suna fassara bisa ga maꞌanar, wato suna amfani da kalmomin nasu yaren don su fassara abin da wurin ya ce a ainihin yare da aka rubuta shi.

  •   Wasu sukan takaita abin da Baibul ya fada da nasu yaren don su sa mutanensu su ji dadin karanta Baibul. Sai dai wani lokaci, garin sa fassarar ta yi dadi, sukan fadi wani abu dabam da ba ainihin abin da ake nufi ba.

 Fassara mai kyau tana bin ainihin kalmomin da aka yi amfani da su, tana kuma amfani da yadda mutane suke magana a zamaninmu don ta maimaita ainihin abin da Allah ya fada, yadda mutane za su fahimta. e

 Waye ne ya umurta abin da aka rubuta a Baibul?

 Tun da Baibul na Allah ne, shi ne ya zabi abin da yake so kuma ya sa aka rubuta a ciki. A dā, Israꞌilawa ne ya ba su hakkin kula da “Rubutacciyar Maganar Allah mai tsarki.”​—Romawa 3:2.

 Akwai littattafan da ya kamata a hada su a Baibul, amma ba sa ciki?

 Aꞌa. Duka littattafan suna ciki; babu waninsu da ba a saka ba. Wasu suna ganin akwai wasu kananan littattafai na zamanin dā, da ake da su a yau da ya kamata a ce suna cikin Baibul. f Amma Baibul yana da koyarwarsa wadda za a iya amfani da ita don a san gaskiyar. (2 Timoti 1:13) Idan aka duba koyarwar Baibul, za a ga cewa duka littattafan da Allah ya sa aka rubuta sun jitu da juna. Amma duka sauran littattafan nan da mutane suke ganin cewa ya kamata a hada su a Baibul, ba su da wannan jituwar. g

 Yadda za ka nemi ayoyi a cikin Baibul

  Sunayen littattafan da ke cikin Baibul

a Idan kana son ka ga sunayen dukan littattafan da ke cikin Baibul, da wadanda suka rubuta su da kuma lokacin da aka rubuta kowannensu, ka duba talifin nan “Table of the Books of the Bible” da Turanci.

b Akwai wasu nassosin da ke cikin Baibul da asalinsu an rubuta su da wani yare ne da ke kama da Ibrananci, ana kiransa Aramaic.

c Mutane da yawa da suke karanta Baibul sun fi son kiransa da “Nassosin Ibrananci” da kuma “Nassosin Helenanci na Kirista.” Domin idan aka ce “Tsohon Alkawari” da “Sabon Alkawari” yakan sa a ga kamar “Tsohon Alkawarin” bai da amfani kuma, ko a ga kamar “Sabon Alkawarin” ya dauki matsayinsa.

e Mutane da yawa suna jin dadin karanta juyin New World Translation of the Holy Scriptures domin an bi ainihin abin da Baibul ya ce a fassarar kuma yana da saukin karantawa. Domin karin bayani ka karanta talifin nan “Is the New World Translation Accurate?” da Turanci

f Kananan littattafan nan su ne ake kira littattafan Apocrypha. Littafin tarihi mai suna Encyclopædia Britannica, ya ce “a batun rubucce-rubuccen Baibul, [kalmar nan Apocrypha tana nufin] littattafan da ba a amince da su cewa suna cikin ainihin nassosi ba.” Wato ba sa cikin jerin kananan littattafan da Allah ya sa aka rubuta da suke cikin Baibul.

g Don samun karin bayani, ka karanta talifin nan “Apocryphal Gospels​—Hidden Truths About Jesus?” da Turanci