Koma ka ga abin da ke ciki

Tsoron Mutuwa, Ta Yaya Zan Shawo Kansa?

Tsoron Mutuwa, Ta Yaya Zan Shawo Kansa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Ba laifi ba ne mu ji tsoron mutuwa kuma muna iyakacin kokarinmu a tsare kanmu daga haka. (1 Korintiyawa 15:26) Amma irin banzan tsoro na razana da ake yi domin karya ko kuma camfi yana jefa mutane cikin “bauta muddar ransu.” (Ibraniyawa 2:​15) Sanin gaskiya zai ’yantar da kai daga banzan tsoron mutuwa, irin tsoron da ke hana mutum sukuni a rayuwa.​—Yohanna 8:​32.

Gaskiya game da mutuwa

  •   Matattu ba su san kome ba. (Zabura 146:4) Kada ka yi tunani azaba ko ciwo bayan ka mutu, domin Littafi Mai Tsarki ya kwatanta mutuwa da barci.​—Zabura 13:3; Yohanna 11:11-​14.

  •   Matattu ba za su iya mana wani barna ba. Ko magabta a dā ma sun “mutu.” (Misalai 21:16) Littafi Mai Tsarki ya ce “kiyayyarsu, da kishinsu, yanzu sun kare.”​—Mai-Wa’azi 9:6.

  •   Mutuwa ba ita ce karshen rayuwarmu ba sam sam. Allah za ya dawo da mutane da suka mutu ta wurin ta da su zuwa rai.​—Yohanna 5:​28, 29; Ayyukan Manzanni 24:15.

  •   Allah ya yi alkawarin lokacin da “mutuwa kuwa ba za ta kara kasancewa ba.” (Ru’ya ta Yohanna 21:4) Game da ranar nan, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Masu-adalci za su gāji kasan, su zauna a cikinta har abada,” ba za a kara jin tsoron mutuwa kuma ba.​—Zabura 37:29.