Koma ka ga abin da ke ciki

Salama a Duniya​—Ta Yaya Za a Same Ta?

Salama a Duniya​—Ta Yaya Za a Same Ta?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Za a sami salama a duniya ba ta wurin ƙoƙarin mutane ba, amma ta wurin Mulkin Allah, gwamnati ta samaniya da Kristi Yesu ke sarautarsa. Ka lura da yadda Littafi Mai Tsarki ya koya mana game da wannan bege na musamman.

  1.   Allah za ya “sa yaƙoƙi su ƙare har iyakar duniya,” zai cika alkawarinsa “a duniya kuma salama wurin mutanen da ya ke murna da su sarai.”—Zabura 46:9; Luka 2:14.

  2.   Mulkin Allah zai yi sarauta daga sama a bisa dukan duniya. (Daniel 7:14) Da yake gwamnati ce ta duniya, za ta cire wariyar kabila, abin da ke jawo faɗe-faɗe da yawa ke nan.

  3.   Yesu, Sarkin Mulkin Allah, ana ce da shi “Sarkin Salama,” kuma zai tabbata cewa “salama ba ta da iyaka.”—Ishaya 9:6, 7.

  4.   Ba za a bar mutane da suka ƙudura su ci gaba da faɗe-faɗe su kasance cikin Mulkin ba, da yake “mai-mugunta da mai-son zalunci ransa [Allah] yana ƙinsu.”—Zabura 11:5; Misali 2:22.

  5.   Allah yana koya wa talakawansa yadda za su yi zaman salama. Littafi Mai Tsarki ya kwatanta sakamakon wannan koyarwar da ya ce: “Za su kuma bubbuge takubansu su zama garmuna, māsunsu kuma su zama lauzuna: al’umma ba za ta zāre wa al’umma takobi ba, ba kuwa za a ƙara koyon yaƙi nan gaba ba.”—Ishaya 2:3, 4.

 Miliyoyin Shaidun Jehobah a duniya duka suna koyo daga wajen Allah yadda za su kasance da salama. (Matta 5:9) Ko da yake mun fito daga kabilai dabam dabam a ƙasashe sama da 230, ba za mu kashe kowa ba.

A yau Shaidun Jehovah suna koyon hanyoyin samun salama