Koma ka ga abin da ke ciki

Mene ne Ma’anar Kalmar Nan Baftisma?

Mene ne Ma’anar Kalmar Nan Baftisma?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Kafin a ce mutum ya yi baftisma sai an tsoma shi a cikin ruwa kuma ya fito. a Hakan ya nuna mana dalilin da ya sa aka yi wa Yesu baftisma a cikin kogi. (Matta 3:​13, 16) Hakazalika, mutumin Habasha da Filibus “suka shiga ruwa” don a yi wa mutumin baftisma.​—Ayyukan Manzanni 8:​36-40.

Ma’anar baftisma

 A cikin Littafi Mai Tsarki, an kwatanta baftisma da binne mutum. (Romawa 6:4; Kolosiyawa 2:12) Baftisma alama ce da ke wakiltar binne ko kuma kawar da halaye marasa kyau da mutum yake da su a dā sa’an nan ya soma rayuwa a matsayin Kirista da ya kebe kansa ga Allah. Yin baftisma da kuma kebe kai ga Allah abubuwa ne da Allah ya tanadar mana don mu iya kasancewa da lamiri mai kyau, idan mun ba da gaskiya ga hadayar Yesu. (1 Bitrus 3:21) Saboda haka, Yesu ya ce wajibi ne mabiyansa su yi baftisma.​​—Matta 28:​19, 20.

Shin, baftisma tana wanke zunubai?

 A’a. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa ta wurin jinin Yesu ne kawai za a iya wanke ko yafe mana zunubanmu. (Romawa 5:​8, 9; 1 Yohanna 1:7) Kafin mutum ya amfana daga hadayar Yesu, wajibi ne ya ba da gaskiya ga Yesu kuma ya soma yin rayuwar da ta jitu da koyarwar Yesu, sa’an nan a yi masa baftisma.​​—Ayyukan Manzanni 2:38; 3:19.

Littafi Mai Tsarki ya goyi bayan yi wa jarirai baftisma?

 A’a. Ba wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki da ya nuna cewa ya kamata a yi wa jarirai baftisma. A wasu coci ana yi wa jarirai “baftisma” (ta wurin yayyafa musu ruwa a kai) kafin a ba su suna. Mutanen da suka fahimci “bisharar . . . Mulkin Allah” kuma suka yarda da hakan ne ake musu baftisma a matsayin Kiristoci na gaskiya. (Ayyukan Manzanni 8:12) Hakan ya kunshi koyan abin da ke cikin Littafi Mai Tsarki da amincewa da shi da kuma tuba daga abubuwan da mutum yake yi da ba su jitu da nufin Allah ba. Jariri ba za iya yin abubuwan nan ba.​​—Ayyukan Manzanni 2:​22, 38, 41.

 Kari ga hakan, Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah yana daukan yaran Kiristoci da tsarki bisa ga aminci ko bangaskiyar iyayensu. (1 Korintiyawa 7:14) Da a ce yi wa jarirai baftisma zai iya taimaka musu, da Littafi Mai Tsarki bai ce bangaskiyar iyayensu ne zai tsarkaka su ba. b

Ra’ayoyin da ba su dace ba game da baftisma

 Karya: Za a iya yayyafa ko zuba wa mutum ruwa maimakon a tsoma shi a cikin ruwa.

 Gaskiya: Duka wadanda aka yi musu baftisma da aka ambata a cikin Littafi Mai Tsarki, an tsoma su ne a cikin ruwa. Alal misali, a lokacin da Filibus ya yi wa wani mutumin Habasha baftisma, sai da “suka shiga ruwa.” Bayan da suka gama baftisma sai ‘suka fito daga cikin ruwan.’​—Ayyukan Manzanni 8:​36-39. c

 Karya: Da yake Littafi Mai Tsarki ya ce an yi wa iyalai gaba daya baftisma, hakan ya nuna cewa an yi wa jariran gidan ma baftisma ke nan. Alal misali, game da wani mai tsaron kurkuku a Filibi Littafi Mai Tsarki ya ce: sai “aka yi masa baftisma da dukan iyalinsa.”​—Ayyukan Manzanni 16:​31-34.

 Gaskiya: Abin da aka fada a wannan ayar ya nuna cewa wadanda aka yi musu baftisma sun fahimci “maganar Allah” kuma suka yi “murna da gaske.” (Ayyukan Manzanni 16:​32, 34) Wadannan dalilan sun nuna cewa ba a yi wa wani jariri baftisma a gidan ba, domin jarirai ba za su iya fahimtar maganar Allah ba.

 Karya: Yesu ya nuna cewa ya kamata a rika yi wa jarirai baftisma domin ya ce Mulkin Allah na yara kankanana ne.​​—Matta 19:​13-15; Markus 10:​13-16.

 Gaskiya: Ba batun baftisma ne Yesu yake tattaunawa a lokacin da ya yi wannan furucin ba. Yana koya wa almajiransa ne cewa kafin mutum ya sami shiga cikin Mulkin Allah, wajibi ne ya mayar da kansa kamar yaro, wato ya kasance da tawali’u da kuma saukin kai.​​—Matta 18:4; Luka 18:​16, 17.

a A Helenanci, kalmar nan “baftisma” tana nufin “tsomawa.” Ka duba littafin nan, Theological Dictionary of the New Testament, na I, shafi na 529.

b Littafin nan The International Standard Bible Encyclopedia ya ce “babu inda aka rubuta a cikin [Sabon Alkawari] cewa ya kamata a yi wa jarirai baftisma.” Ya kara da cewa, ana yin hakan ne don “yadda mutane suka dauki yin baftisma,” suna gani kamar yin baftisma zai share zunubansu.​​—na 1, shafuffuka na 416-​417.

c A cikin littafin nan, New Catholic Encyclopedia, a karkashin jigon nan “Baftisma (a cikin Littafi Mai Tsarki),” an rubuta cewa: “A bayyane yake cewa Kiristoci na fari sun yi baftisma ta wurin tsoma mutum a cikin ruwa.”​—Na 2, shafi na 59.