Koma ka ga abin da ke ciki

Me Ya Sa Mutane Ke Mutuwa?

Me Ya Sa Mutane Ke Mutuwa?

Amsar Littafi Mai Tsarki

 Idan muka yi rashin wani, yana da sauki mu soma tunanin abin da ya sa mutane ke mutuwa. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Karin mutuwa zunubi ne.”​—1 Korintiyawa 15:56.

Me ya sa dukan mutane suke zunubi kuma suke mutuwa?

 Mutane na farko, Adamu da Hawwa’u sun mutu saboda sun yi zunubi ga Allah. (Farawa 3:17-19) Mutuwa ce kawai sakamakon tawayen da suka yi wa Allah, domin a gare shi ne “mabulbular rai ta ke.”​—Zabura 36:9; Farawa 2:17.

 Dukan zuriyar Adamu sun sami illar zunubin da ya yi. Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zunubi ya shigo cikin duniya ta wurin mutum daya, mutuwa kuwa ta wurin zunubi; har fa mutuwa ta bi kan dukan mutane, da yake duka sun yi zunubi.” (Romawa 5:12) Dukan mutane suna mutuwa domin sun yi zunubi.​—Romawa 3:23.

Yadda za a kawar da mutuwa

 Allah ya yi alkawarin cewa zai “haɗiye mutuwa har abada.” (Ishaya 25:8) Kafin a kawar da mutuwa, dole ne a cire tushenta, wato zunubi. Allah zai yi wannan ta wurin Yesu Kristi, wanda ‘ya dauke zunubin duniya!’​—Yohanna 1:29; 1 Yohanna 1:7.