Koma ka ga abin da ke ciki

Ina Ne Iblis Yake Zama?

Ina Ne Iblis Yake Zama?

Amsar da Littafi Mai Tsarki ya ba da

 Da yake Iblis ruhu ne, ’yan Adam ba sa iya ganinsa. Amma, baya cikin wutar jahannama wajen da yake wahal da miyagun mutane, kamar yadda aka nuna a hoton da ke biye da wannan talifin.

‘Yaki a sama’

 An kyale Shaidan Iblis ya rika yawo a sararin sama, har ma an ba shi damar shiga wurin da Allah da kuma amintattun mala’iku suke. (Ayuba 1:6) Littafi Mai Tsarki ya annabta cewa za a yi ‘yaki a sama,’ a sakamakon haka, za a kore shaidan daga sama kuma a “jefar da shi a duniya.” (Ru’ya ta Yohanna 12:7-9) Yadda abubuwa suka auku bi da bi da aka rubuta a Littafi Mai Tsarki da kuma abubuwan da suke faruwa a duniya sun nuna cewa an riga an yi wannan yakin. Hakan ya sa Iblis bai da ikon komawa sama.

 Shin hakan yana nufi cewa Iblis yana zama a wani wuri ko gari ne a cikin duniya? Alal misali, an ce a birnin Birgamos na dā ne “mazaunin sarautan Shaitan yake” kuma a wurin ne “Shaidan ke zaune.” (Ru’ya ta Yohanna 2:13) Kila an yi wadannan furucin ne domin irin bauta da yawancin mutane suke yi a wannan birnin da yake da alaƙa da shaidan. Littafi Mai Tsarki ya ce Iblis yana sarauta bisa “dukan mulkokin duniya,” saboda haka, ba ya zama a wani wuri ko gari a duniya amma yana yawo ne kawai a cikin duniya.—Luka 4:5, 6.