Koma ka ga abin da ke ciki

Iyayena Suna Shirin Kashe Aure

Iyayena Suna Shirin Kashe Aure

Abin da za ka iya yi

 Ka tattauna damuwarka da su. Ka gaya wa iyayenka yadda zancen ke sa ka bakin ciki ko kuma damunka. Kila za su iya bayyana maka abin da ke faruwa kuma hakan zai sa zuciyarka ta dan kwanta.

 Idan iyayenka ba sa iya taimaka maka, sai ka yi magana da wani aboki da ya manyanta.—Misalai 17:17.

 Fiye da haka ma, za ka sami wanda zai saurare ka, Ubanka na sama, “mai-jin addu’a.” (Zabura 65:2) Ka fada masa abin da ke zuciyarka “domin yana kula da” kai.—1 Bitrus 5:7.

Abin da ba za ka yi ba

Shawo kan bakin ciki saboda da kashe aure da iyayenka suka yi yana kama da samun sauki sa’ad da ka karye, wato, hakan na da zafi sosai amma zai warke daga baya

 Kada ka rike su a zuciya. “Iyayena masu son kai ne,” in ji Daniel, wanda iyayensa suka rabu sa’ad da yake dan shekara bakwai. “Ba su damu da mu ba sam kuma ba su yi tunanin yadda abin da suka yi zai shafe mu ba.”

 Me zai faru da Daniel idan ya ki daina yin fushi da bakin cikin nan—Taimako: Karanta Misalai 29:22.

 Me ya sa yake da kyau Daniel ya yi kokarin gafarta wa iyayensa domin bata masa rai da suka yi?—Taimako: Karanta Afisawa 4:31, 32.

 Ka guje wa halin da zai halakar da kai. “Bayan da iyayena suka kashe aure, na yi bakin ciki kwarai,” in ji Denny. “Na soma samun matsala a makaranta kuma a shekarar ban ci jarrabawa ba. Bayan haka ... na zama dan iskan ajin kuma nakan yi fada sosai.”

 Me kake tsammanin Denny yake neman ya cim ma ta wurin zama dan iskan ajinsa da kuma yawan fadace-fadacen da yake yi?

 Ta yaya ka’idar da ke Galatiyawa 6:7 zai taimaka wa mutane irinsu Denny su guje wa halin da zai halakar da su?

 Irin bakin ciki da kashe aure yake haifarwa ba ya wucewa da sauri. Amma sa’ad da rayuwarka ta soma dan daidaitawa sai ka soma samun hankalinka.