Koma ka ga abin da ke ciki

TAIMAKO DON IYALI | RENON YARA

Yara da Waya​—Sashe na 1: Shin Ya Kamata In Ba Dana Babban Waya?

Yara da Waya​—Sashe na 1: Shin Ya Kamata In Ba Dana Babban Waya?

 A yau, yara da yawa suna da wayar selula, a kuma da yawa daga cikinsu suna amfani da intane ta wayarsu a dakunansu. Wadanne hadarurruka ne ke tattare da barin yara su rika amfani da manyan wayoyin selula? Mene ne amfanin samun babbar waya? Har tsawon wane lokaci ne ya kamata ka bar yaranka su rika amfani da wayar selula a kowace rana?

 Abin da ya kamata ka sani

 Amfanin manyan wayoyi

  •   Yara za su sami kāriya, iyaye za su kasance da kwanciyar hankali. Wata mai suna Bethany da take da yara biyu ta ce: “Muna rayuwa a duniyar da ke cike da mugunta. Yana da muhimmanci yara su iya kiran iyayensu a waya in ba sa tare.”

     Wata mahaifiya mai suna Catherine ta ce: “Akwai wasu manhaja da mutum zai iya sakawa a wayar ’yarsa ko dansa don ya san inda yake. Idan yana tuki, za ka ma iya sanin ko yana gudu sosai.”

  •   Yana taimakawa da aikin makaranta. Wata mahaifiya mai suna Marie ta ce: “Ana tura wa yara aikin makaranta ta imel ko kuma ta sakonnin tes, kuma suna yin amfani da waya domin su tattauna da malamansu.”

 Hadarurruka

  •   Bata lokacin a yin amfani da waya. Yawancin matasa suna yin amfani da wayoyinsu na sa’o’i da yawa a kowace rana. Ko iyaye ma suna cin lokaci a yin amfani da wayoyinsu fiye da yadda suke tattaunawa da yaransu. Don haka, wani mai ba da shawara ya ce “yawancin iyalai ba sa tattaunawa da juna, sun fi mai da hankali ga na’urorinsu.” b

  •   Batsa. Wani bincike ya nuna cewa fiye da rabin matasa masu shekaru 13 zuwa 19 sukan kalli batsa kowace wata domin yana da sauki su kalla ta waya. Wani mahaifi mai suna William da ke da matasa biyu ya ce: “Idan iyaye suka ba yaransu waya, kamar dai sun bude musu hanyar kallon batsa a duk inda suke ne.”

  •   Shakuwa. Mutane da yawa suna shakuwa da wayoyinsu sosai. Sun ce idan ba su ga wayarsu ba sukan damu, su rasa abin da za su yi ko kuma su soma rashin lafiya. Wasu iyaye sun ce sa’ad da yaransu suke amfani da waya sukan yi taurin kai sosai. Wata mai suna Carmen ta ce: “A wasu lokuta, idan ina yi wa dana magana, sai ya harare ni ko kuma ya yi mini bakar magana domin ba ya so in dame shi.”

  •   Wasu karin hadarurruka. Ana iya cin zalin yaran da suke amfani da waya ta intane kuma a tura musu hotuna da sakonnin batsa. Rashin zama da kyau da rashin barci yayin da ake amfani da waya zai iya jawo wa yara rashin lafiya. Wasu yara suna da hanyoyin boye abubuwa marasa kyau da ba sa so iyayensu su gani a cikin wayoyinsu. Alal misali, za su iya ba ma wani manhaja mai illa suna da zai sa a ga kamar manhajar ba ta da illa, kamar manhajar lissafi don su boye wa iyayensu.

     Daniel, mahaifin wata matashiya ya ce: “Manyan wayoyi suna bude wa yara hanyar yin kome da kuma ganin kome a intane, ko da abu mai kyau ne ko marar kyau.”

 Tambayar da ya kamata ka yi

  •   ‘Shin dana yana bukatar babbar waya?’

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Mai hankali yakan yi tunani kafin ya fara wani abu.” (Karin Magana 14:15) Don haka, ka tambayi kanka:

     ‘Dana yana bukatar babbar waya saboda rashin tsaro ko wasu dalilai dabam? Anya, na yi tunanin amfani da kuma hadarurrukan da ke tattare da babbar waya? Shin zai iya amfani da karamar waya maimakon babba?’

     Wani mahaifi mai suna Todd ya ce: “Akwai kananan wayoyi da za ka iya saya wa yaranka da za ka iya kiransu ko tura musu sako a ciki. Kuma wadannan wayoyin ba su da tsada.”

  •   ‘Dana zai iya cika hakkinsa na yin amfani da babbar waya?’

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Zuciyar mai hikima takan kai shi ga yin abin da yake daidai.” (Mai-Wa’azi 10:2) Saboda haka, ka tambayi kanka:

     ‘Me ya sa na yarda da dana? Shin ya saba gaya mini abin da ke zuciyarsa? Yana boye mini wasu abubuwa, alal misali abokansa? Yana nuna kamun kai a yadda yake amfani da na’urori kamar su talabijin ko kwamfuta?’ Wata mahaifiya mai suna Serena ta ce: “Babbar waya tana da amfani sosai amma tana da hadarurruka ma. Ka yi tunanin irin babban aikin da kake ba danka tun bai gama girma ba.”

  •   ‘A shirye nake in dauki nauyi?’

     Littafi Mai Tsarki ya ce: “Koyar da ’ya’yanka cikin hanyar da za su bi.” (Karin Magana 22:6) Don haka, ka tambayi kanka:

     ‘Na san yadda ake amfani da waya sosai don in taimaka wa dana ya san hadarurruka da ke tattare da yin amfani da waya kuma ya guje musu? Na san yadda zan saita wayar don in sami izinin sanin inda dana yake shiga a cikin wayar? Ta yaya zan taimaka wa dana ya san abubuwan da zai rika kallo a waya?’ Daniel, mahaifin da aka yi kaulinsa a baya ya ce: “Ina ganin iyaye da yawa suna ba yaransu manyan wayoyi sai su bar yaran su yi abin da suka ga dama da wayar.”

 Gaskiyar batun: Yara suna bukatar a koyar da su don su san yadda za su yi amfani da manyan wayoyi a hanya mai kyau. Wani littafi mai jigo Indistractable, ya ce: “Yana da sauki yara su yi amfani da waya fiye da yadda ya kamata musamman idan iyayensu ba su damu da su ba.”

a A wannan talifin, “babbar waya” tana nufin wayar da za ta iya shiga intane.

b Daga littafin nan Disconnected wanda Thomas Kersting ya wallafa.